'Abin da Ya Sa Tinubu Zai Ci Zaben 2027': Kwankwaso Ya Magantu, Ya Tabo Maganar Ganduje

'Abin da Ya Sa Tinubu Zai Ci Zaben 2027': Kwankwaso Ya Magantu, Ya Tabo Maganar Ganduje

  • Shugaban hukumar kula da kogunan Hadejia Jama’are, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce 'yan Najeriya za su sake zaben Bola Tinubu
  • Hon. Kwankwaso ya ce Tinubu ya samar abubuwan more rayuwa a yankin wanda ya cancanci a sake ba shi dama a shekarar 2027
  • Ya soki wasu 'yan Arewa da ya ce ba su yi komai don ci gaban yankin ba, yana mai cewa lokaci ya yi da za su bar son kai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kula da kogunan Hadejia Jama’are, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi magana kan gwamantin Bola Tinubu.

Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin da zai sa ‘yan Najeriya su sake zaben Shugaban kasa Bola Tinubu a shekarar 2027.

Kwankwaso ya magantu kan sake zaben Tinubu a 2027
Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce babu abin da zai hana Bola Tinubu samun nasara a 2027. Hoto: Musa Ilyasu Kwankwaso, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Musa Kwankwaso ya magantu kan zaben Tinubu

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi laifin da Tinubu ya yi wa manyan Arewa

Jigon APC ya goyi bayan kalaman shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ce babu gurbi a fadar shugaban kasa har sai 2031, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kwamishinan a Kano ya ce ko da ba tare da goyon bayan Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ba, Tinubu zai samu nasara.

“Babu wani tasirin siyasa da zai hana Tinubu samun kuri’u masu yawa a Arewacin Najeriya a zaben 2027.

- Musa Ilyasu Kwankwaso

2027: Kwankwaso ya yaba da maganar Ganduje

Da yake mayar da martani kan suka da wasu suka yi wa matsayar Ganduje, Kwankwaso ya ce:

“Arewa ta jira har sai 2031 kafin ta sake neman mulki, yawancin wadanda ke cikin Kungiyar Arewa sun yi shekaru a mulki amma me suka yi don ceto Arewa?"
“Mutane irin su Solomon Dalung, Najaatu Muhammad, da Dr Rabiu Musa Kwankwaso ba su da abin fada ga Arewa saboda ba za su iya nuna abin da suka yi wa yankin ba.

Kara karanta wannan

Matawalle ya tsoma baki da Canada ta wulakanta Najeriya, ya fadi matakin da za su dauka

“Matsayar Ganduje cewa gudunmuwar Tinubu a Arewa cikin ‘yan watannin mulkinsa ta fi tasiri fiye da na wasu da ba su da abin nuna wa tarihi."

Kwankwaso ya ce a duk Arewacin Najeriya ana ayyuka daban-daban kuma duk wannan aikin Tinubu ne, kuma za a ci gaba da ayyukan idan ya sake komawa mulki a 2027.

The Nation ta ce Kwankwaso ya yaba wa Ganduje kan salon jagorancinsa, yana mai cewa:

“Mun ga yadda ya lashe jihohi da dama a zaben gwamna da kuma yadda ‘yan majalisar kasa ke komawa APC.

Musa Kwankwaso ya caccaki Naja'atu Muhammad

Kun ji cewa shugaban kula da kogunan Hadejia Jama’are, Musa Ilyasu Kwankwaso ya tabo Naja'atu Muhammad, inda ya zarge ta da cin mutuncin manyan ‘yan siyasa.

Kwankwaso ya ce Naja'atu ta kware a sukar shugabannin Najeriya tun zamanin Obasanjo har zuwa Jonathan da Atiku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.