Ana tsakiyar Rikicin El Rufai da Uba Sani, 'Yan Majalisa 3 Sun Fice daga PDP zuwa APC
- Wasu 'yan majalisar dokokin jihar Kaduna uku da aka zaba a jam'iyyar PDP sun sanar da cewa sun sauya sheka zuwa APC
- Henry Mara, Emmanuel Kantiok, da Samuel Kambai sun ce ci gaban al'ummarsu da Gwamna Uba Sani ne silar sauya shekar
- 'Yan majalisar sun ce nasarorin Uba Sani cikin shekaru biyu sun kawo zaman lafiya da ci gaba, tare da rage tasirin 'yan adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - 'Yan majalisar ddokokin Kaduna uku da aka zaba karkashin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC tare da magoya bayansu.
'Yan majalisar da suka sauya shekar sun hada da Henry Mara (Jaba), Emmanuel Kantiok (Zonkwa) da Samuel Kambai (Zango).

Asali: Facebook
'Yan siyasar sun sanar da sauya shekarsu ne a ranar Alhamis a mazabunsu daban-daban, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan majalisar Kaduna 3 sun fice daga PDP
A wata hira ta wayar tarho, 'yan majalisar sun ce sun yanke shawarar sauya sheka ne don su hada kai da gwamnatin jiha.
Sun ce wannan matakin yana da nasaba da jagorancin Gwamna Uba Sani da kuma nasarorin da ya samu a mulkinsa.
Sauya shekarsu na zuwa ne bayan dan majalisar tarayya mai wakiltar Zangon Kataf/Jaba, Amos Magaji, ya koma APC.
Dalilin sauya shekar 'yan majalisar zuwa APC
Hon. Mara ya bayyana cewa tasirin PDP a Kudancin Kaduna ya ragu sosai cikin 'yan kwanakin nan.
“Nan ba da jimawa ba, za a iya ganin karin ‘yan adawa da za su sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC,” inji Hon. Mara.
Hon. Samuel Kambai ya ce nasarorin Uba Sani sun kawar da gaba tsakanin jama’a da jam’iyyar mai mulki a jihar.

Kara karanta wannan
Siyasar Kano ta rikice: Kusoshin NNPP sun watsar da Kwankwaso, sun kama layin APC
“Nasarorin Gwamna Uba Sani cikin shekaru biyu sun kawo karshen tasirin jam’iyyun adawa a jihar,” inji Hon. Kambai.
"Uba Sani ya kawo zaman lafiya" - Hon. Kantiok
Hon. Kambai ya bayyana cewa tun 1999 Kudancin Kaduna na karkashin PDP amma jagorancin Gwamna Uba Sani ya sauya wannan tarihi.
Hon. Kantiok ya ce jihar ta fuskanci matsalolin tsaro a baya amma yanzu an samu zaman lafiya, yana mai alkawarin ci gaba da goyon bayan Gwamna Sani.
Ya kara da cewa matsayar su ita ce yin aiki don ci gaban al’ummarsu ta hanyar zama cikin jam’iyyar mai mulki.
Kaduna: Dan majalisar tarayya ya fice daga PDP
A wani labarin, mun ruwaito, cewa, Hon. Amos Magaji, dan majalisar wakilai na mazabar Zangon Kataf/Jaba, a Kaduna ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Hon. Magaji ya ce rikice-rikicen PDP daga matakin ƙasa zuwa mazabu ne suka tilasta masa barin jam'iyyar, ganin ba zai iya ci gaba da kasancewa a cikinta ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng