"Ka Yi Mubaya'a," Sanatan da El Rufa'i Ya Tsinewa Ya Ce Tsohon Gwamna Ya Daina Ja da Uba Sani

"Ka Yi Mubaya'a," Sanatan da El Rufa'i Ya Tsinewa Ya Ce Tsohon Gwamna Ya Daina Ja da Uba Sani

  • Suleiman Othman Hunkuyi ya shawarci tsohon gwamna Nasir El-Rufai da ya amince da Gwamna Uba Sani a matsayin sabon jagora a Kaduna
  • Hunkuyi ya bukaci El-Rufa’i da ya nemi gafarar Allah da kuma bai wa mutanen Kaduna hakuri kan abubuwan da ake zarginsa da aikatawa
  • Hunkuyi ya kuma shawarci El-Rufa’i da ya nemi gafarar shugabannin jam’iyyar APC da ya taba bayyana su a matsayin jahilai da yake kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Wani jigo a jam’iyyar APC a Kaduna, Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, ya shawarci tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, da ya goyi bayan magajinsa, Sanata Uba Sani a matsayin shugaban jihar na yanzu.

Ya kuma bukaci El-Rufai da ya nemi yafiyar mutanen Kaduna kan abin da ake zarginsa da aikatawa a lokacin da ludayinsa ke kan dawo.

Kara karanta wannan

APC ta shawarci El-Rufa'i a kawo ƙarshen takun saka da gwamnatin Tinubu

Rufai
An shawarci El Rufa'i kan rikici da Uba Sani Hoto: Uba Sani, Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Hunkuyi, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta Arewa Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019 karkashin APC, ya samu sabani da El-Rufai a lokacin gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'El-Rufa’i ya daina adawa da Uba Sani' - Hunkunyi

Da yake jawabi a wani taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga Zariya, Sanata Hunkuyi ya nemi El-Rufai ya daina adawa da Gwamna Uba Sani da kuma shugabancin jam’iyya.

Ya bayyana cewa tsohon gwamnan ba shi da wani zabi sai ya amince da goyon bayan Gwamna Sani a matsayin sabon jagoran jihar Kaduna.

A cewarsa:

“Na dauki tsawon shekaru biyu ina azumin magana a bainar jama’a. Na nisanci kafofin yada labarai, kuma babu wanda ya tilasta mini yin hakan, na dauki wannan shawarar ne da kaina. Amma yanzu lokaci ya yi da zan bude bakin.”

Hunkuyi ya bukaci El-Rufa’i ya nemi gafarar Allah

Kara karanta wannan

Tinubu: Dan majalisa ya hada Ganduje da El Rufa'i, ya gyara musu zama kan 2027

Sanata Suleiman Hunkuyi ya kuma bukaci El-Rufai da ya nemi gafarar Allah, kuma ya ba mutanen Kaduna hakuri saboda abubuwan da ya aikata yayin da yake mulki.

Hunkuyi ya nanata cewa yanzu da Gwamna Uba Sani ya samu nasara a zabe, El-Rufai ya kamata ya bi shi don zaman lafiya.

Sanatan ya kuma shawarci tsohon gwamnan da ya nemi gafara daga shugabannin jam’iyyar da ya taba bayyana su a matsayin jahilai.

Nasir El-Rufa'i ya samu goyon bayan MURIC

A wani labarin, mun wallafa cewa kungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya, MURIC, ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta tozarta tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

MURIC ta bayyana cewa yin haka zai ɓata sunan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a idon duniya, musamman idan har akwai gaskiya a rade-radin da ake yi cewa ana shirin kama tsohon gwamnan.

Ƙungiyar ta ce tozartawa ko muzgunawa tsohon gwamnan Kaduna ba zai nuna dimokuraɗiyya ba, ganin yadda Malam Nasir El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar zAPC a shekarar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.