Yadda Kwankwaso Ya Fara Gana wa da Manyan 'Yan Siyasa gabanin Zaben 2027

Yadda Kwankwaso Ya Fara Gana wa da Manyan 'Yan Siyasa gabanin Zaben 2027

Tun a shekarar 2024, tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ke ganawa da wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewa da Kudu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wadannan tattaunawa, musamman ta baya-bayan nan sun janyo ce-ce-ku-ce, inda ake ganin suna da alaka da shirin Kwankwaso na fadada tasirinsa a siyasar Najeriya.

Kwankwaso
Ana zaton Kwankwaso ya fara shirin zaben 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Hon Nanu Kankarofi
Asali: Facebook

Legit ta tattaro ganawar da Sanata Kwankwaso ya yi da manyan 'yan siyasa uku a Najeriya, da kuma yadda masana harkokin siyasa ke kallon lamarin.

1. Ganawar Rabiu Kwankwaso da Rauf Aregbesola

Jaridar Daily Trust a watan Fabrairu, 2025, Jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya gana da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, a Legas.

Kara karanta wannan

Majalisa: "Matasa sama da 500,000 a jihohin Arewa 2 sun rasa aikin yi"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattaunawar da aka yi bayan an sa labule tsakanin manyan ƴan siyasa biyu, ta jawo hasashen yiwuwar hadin gwiwa ko wata alaka ta siyasa a tsakaninsu gabanin zaben 2027.

The Nation ta wallafa cewa Aregbesola, wanda APC ta kora a watan Janairu 2025, na da matukar tasiri a siyasar yankin Kudu maso Yamma, musamman a jihohin Osun da Legas.

2. Ziyarar Kwankwaso ga Olusegun Obasanjo

A watan Disamba 2024, Kwankwaso ya kai ziyara ga tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, da rakiyar tsohon gwamnan Kuros Ribas, Donald Duke.

Kwankwaso
An yi hasashen Kwankwaso da Obasanjo sun tattauna matsalar ƙasa Hoto: Hon Nunu Kankarofi
Asali: Facebook

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar tasu ta mayar da hankali kan batutuwan kasa, ciki har da makomar siyasa da shugabanci a Najeriya da makomar ƴan ƙasa.

3. Kwankwaso ya sa labule da El-Rufa'i

Leadership ta ruwaito cewa jagoran Kwankwasiyya a Najeriya, Sanata Kwankwaso ya gana da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, a Abuja a watan Yuni ta 2024.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

Kwankwaso
Ana zaton ganawar Kwankwaso da El-Rufa'i a 2024 na son wargaza shirin Tinubu a 2027: Rabiu Musa Kwankwaso/Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Ana ganin wannan yunkuri wani bangare ne na kokarin kulla kawance ta siyasa a Arewacin Najeriya, wanda ka iya zama barazana ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Yadda APC ke kallon shirin Kwankwaso

Sakataren yaɗa labaran APC, reshen jihar Kano, Ahmed S Aruwan ya shaida wa Legit cewa ba sa fargabar hadewar wasu manyan ƴan siyasa a Najeriya.

Kwankwaso
APC ta ce ba ta jin ziyarar Kwankwaso ga ƴan siyasa Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Ya kara da cewa:

"Kwankwaso ma ba shi da jam'iyya yanzu, wannan shi ne babban kalubalen da ya ke gabansa, in ma ya tafi (gana wa da ƴan siyasa), ya tafi neman ina ne zai maƙale."
"Duk da dai an ce yana ta bibiya ya ga ta inda zai bi (ya shiga APC), amma mu a matsayinmu na jam'iyya ba wanda ya mana magana, ba mu san da magana ba."
Ya jaddada cewa ba sa buƙatar Sanata Kwankwaso ya shiga APC, domin ba sa buƙatar Kwankwaso wajen yin nasara a zaben 2027."

Kara karanta wannan

NNPP: "Har yanzu Kwankwaso, Abba halastattun 'yan jam'iyya ne"

Ra'ayin masana a kan ganawar ƴan siyasa

A bangaren masana harkokin siyasa irinsu Dr. Saidu Ahmad Dukawa, ya shaida wa majiyar Legit cewa abubuwa biyu ne ke sa ƴan siyasa ziyarar juna.

Dr. Dukawa, wanda shi ne Sakataren zauren majalisar malamai na jihar Kano ya ce wanna na nuna ko dai ƙulla ƙawancen siyasa, ko karkato da hankalin jam'iyya mai mulki ta neme su.

Kwankwaso ya ƙara samun goyon baya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Bishof Isaac Idahosa ya ce har yanzu, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso me jagoran jam'iyya.

Ya bayyana haka ne a lokacin da rikicin shugabanci ke kokarin kunno kai a cikin NNPP, sai dai Bishof Idahosa ya ce masu takaddamar shugabanci korarrun ƴan jam'iyya ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.