El Rufa'i Ya Samu Goyon bayan Ƙungiyar Musulunci a Faɗansa da Gwamnatin Tinubu

El Rufa'i Ya Samu Goyon bayan Ƙungiyar Musulunci a Faɗansa da Gwamnatin Tinubu

  • Ƙungiyar MURIC mai fafutukar kare haƙƙin musulmi ta gargaɗi gwamnatin tarayya ta guji duk wani abu na muzgunawa Malam Nasir El-Rufai
  • MURIC ta bayyana cewa muzgunawa tsohon gwamnan jihar Kaduna zai ɓata sunan gwamnatin shugaba Tinubu a idon duniya
  • Wannan gargadi na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin gwamnatin Najeriya na shirin kama Malam El-Rufai idan ya dawo Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kungiyar kare haƙƙin Musulmi watau MURIC ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta tozarta tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar jiya, MURIC ta ce yin haka zai ɓata sunan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a idon duniya.

Malam Nasir El-Rufai.
MURIC ta gargaɗi gwamnatin Tinubu kan raɗe-raɗin ana shirin kama tsohon gwamnan Kaduna Hoto: @ElRufai
Asali: Twitter

Ƙungiyar addinin Musuluncin wacce ta yi fice wajen kare haƙƙin Musulmi a Najeriya ta ce muzgunawa El-Rufai ba dimokuraɗiyya ba ce, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dan majalisa ya hada Ganduje da El Rufa'i, ya gyara musu zama kan 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya yi zargin an shirya kama shi

Idan ba ku manta ba, tsohon gwamnan Kaduna ya bayyana cewa ya samu labarin ana shirin kama shi sakamakon sukar da yake yi wa gwamnatin APC.

Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa ba zai gudu ya ɓuya a wasu ƙasashen ba, zai zauna a Najeriya duk abin da zai faru ya faru.

MURIC: "Ka da a muzgunawa Nasir El-Rufai"

Ƙungiyar MURIC ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kada ta bi hanyar tozarta tsohon gwamnan, tana mai cewa El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar APC a zaɓen 2023.

A cewarta, El-Rufai, lokacin yana matsayin gwamnan Kaduna, na ɗaya daga cikin waɗanda suka dage har Tinubu ya zama ɗan takarar APC, kuma ya ci zaɓen shugaban ƙasa.

A sanarwar, MURIC ta ce:

"Idan wannan jita-jita gaskiya ce, muna shawartar gwamnatin tarayya da ta guji muzgunawa tsohon gwamna. Yin haka zai ɓata sunan gwamnatin Tinubu a idon duniya kuma zai nuna cewa tana murƙushe masu adawa da ita."

Kara karanta wannan

Kama Farfesa Usman Yusuf ya ƙara tayar da ƙura, Naja'atu da ministan Buhari sun tona asiri

Kungiyar ta ƙara da cewa barin El-Rufai ya ci gaba da rayuwarsa cikin ‘yanci da tafiya ko’ina da yake so zai tabbatar da mutuncin gwamnatin Najeriya a idon duniya.

Wani ɗan APC kuma mai goyon bayan Tinubu, Aliyu Zaharadeen ya ce duk da Malam Nasiru ya ba da gudummuwa a jam'iyya, ba zai yiwu ya yi ta sakin baki a ƙyale shi ba.

Jigon wanda ke zaune a Kaduna ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa yana mugun ƙaunar El-Rufai amma ba ya jin daɗin yadda yake taba mai girma Tinubu.

Aliyu ya ce:

"Dukkansu mutane na ne a siyasa, a nan Kaduna na fi son Malam Nasiru, to amma ba na jin daɗin yadda yake taba gwamnatin Tinubu a matakin ƙasa.
"Batun kamu kuma duk surutun mutane na ɗauke shi, bana tunanin Tinubu zai kama Malam, kawai dai barazana ce kuma ina da yaƙinin za a warware matsalar."

Kara karanta wannan

'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023

Hadimin Tinubu ya caccaki El-Rufai

A wani rahoton, kun ji cewa mai magana da yawun shugaban ƙasa, Daniel Bwala ya sake sukar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Bwala ya bayyana cewa El-Rufai ba zai iya kayar da shugaban ƙasa ba a zaɓe kuma duk sukar da yake yi wa gwamnatin APC ba ta gaban mai girma Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262