Zaben 2027: Gwamna Ya Fadi Fargabar APC kan Shirin Hadakar 'Yan Adawa
- Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya taɓo batun yiwuwar yin haɗakar jam'iyyun adawa domin tunkarar zaɓen 2027
- Hope Uzodimma ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta da wata fargaba kan ƙulle-ƙullen da ƴan adawan suke yi domin karbar iko
- Shugaban gwamnonin APC ya ce jam'iyyar ba ta tsoron shiga zaɓe kuma ƴan Najeriya ne za su yi mata hukunci a takarar 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Imo kuma shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, Sanata Hope Uzodimma, ya yi magana kan shirin haɗaka na ƴan adawa.
Gwamna Uzodimma ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba ta jin tsoron tarukan da manyan jam’iyyun adawa ke yi a ƙoƙarinsu na shirin zaɓen 2027.

Asali: Twitter
Uzodimma ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi magana ne yayin da kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na ƙasa (NWC) ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Tunmef Global Limited don fara aikin rajistar mambobin jam'iyyar.
Wannan mataki zai bai wa jam’iyyar damar samun cikakkun bayanai game da mambobinta.
Ƴan adawa sun fara yin taro
Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan shugabannin jam’iyyun adawa na tattaunawa kan yiwuwar yin haɗaka domin fuskantar zaɓen 2027.
A ranar Litinin, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya jagoranci tsofaffin gwamnonin jihar Cross River da Sokoto, Lyel Imoke da Aminu Tambuwal, zuwa wajen Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Haka nan, tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya hadu da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a wata ganawa da ake zaton tana da alaƙa da zaɓen 2027.
Wace fargaba APC ke da ita kan zaɓen 2027?
Sai dai Uzodimma ya jaddada cewa jam’iyyar APC ba ta da wata fargaba, yana mai cewa ƴan Najeriya ne za su yankewa jam'iyyar hukunci a zaɓe mai zuwa.
"Ba mu jin tsoron abin da ƴan adawa za su ce. Aikinmu shi ne mu shirya jam’iyyarmu yadda za a girmama ta a duniya. Muna jiran zuwan zaɓe, kuma APC ba jam’iyya ba ce da ke gudun shiga zaɓe."
"Babu wata dimokuradiyya a duniya da ba a yin adawa. Ƴan Najeriya ne za su yanke hukunci wajen zaɓar wanda suke so."
- Gwamna Hope Uzodimma
Shugaban APC ya yabi Tinubu
A yayin bikin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar rajistar mambobin, shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya godewa shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewarsa da shirin.
"A matsayina na shugaban jam’iyya, muna ci gaba da kafa tarihi a siyasarmu."
"Ina son na godewa shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa amincewarsa da wannan tsarin na yin rajistar. Wannan shiri an daɗe ana tunaninsa, amma ba a aiwatar da shi ba sai yanzu."
- Abdullahi Umar Ganduje
Ƴan APC sun yi wa Tinubu alƙawari
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar jam'iyyar APC ta yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu alƙawarin ruwan ƙuri'u a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta ɗaukarwa shugaban ƙasa alƙawarin samar masa da ƙuri'u miliyan huɗu a zaɓen 2027, saboda gamsuwar da ta yi da kamun ludayin mulkinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng