An Taso Gwamna a Gaba kan Nada Tsohon Shugaban APC Ya Jagoranci Hukumar Zabe

An Taso Gwamna a Gaba kan Nada Tsohon Shugaban APC Ya Jagoranci Hukumar Zabe

  • Gwamna Umaru Bago ya nada tsohon shugaban jam'iyyar APC, Jibrin Imam, a matsayin shugaban hukumar zaɓen jihar Neja
  • Gwamna ya kuma nada tsohon sakataren APC, M.A. Liman da tsohuwar kwamishina, Amina Guar a matsayin kwamishinoni
  • Jama'a da 'yan adawa sun nuna damuwa kan nadin 'yan jam'iyya, suna cewa hakan na iya kawo nakasu ga sahihancin zaɓen hukumar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Minna, Niger - Al'umma da dama sun yi martani bayan Gwamna Umaru Bago na Niger ya nada tsohon shugaban APC ta jiha muƙamin a hukumar zabe.

An nada Jibrin Imam ne a matsayin shugaban hukumar zaben jihar (NSIEC) wanda aka yi ta ce-ce-ku-ce.

An taso gwamna a gaba kan nadin mukamai a hukumar INEC
An soki gwamna Umar Bago kan nada jigon APC a hukumar zabe. Hoto: Umar Mohammed Bago.
Asali: Facebook

Gwamna Bago ya yi nade-nade a hukumar zabe

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da nadin ta hannun kakakinsa, Bologi Ibrahim a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Gwamna zai karya farashin abinci warwas saboda azumin watan Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Bago ya kuma nada tsohon sakataren APC na jiha, M.A. Liman sa Amina Guar, tsohuwar kwamishina, da wasu shugabannin jam’iyya a matsayin kwamishinoni.

Mutun daya tilo wanda ba dan jam’iyyar ba shi ne Yahaya Idris Abara wanda kafin wannan nadin ma’aikacin NSIEC ne.

Wasu mazauna jihar sun nuna rashin jin dadi kan nadin ‘yan jam’iyya masu katin domin jagorantar hukumar.

Sun bayyana damuwa cewa irin wannan nadi zai iya shafar sahihancin zaɓen da mambobin jam’iyya za su gudanar.

Yan gwagwarmayar sun caccaki Gwamna Bago

Fitaccen mai fafutuka, Yahaya Mohammed-Usman, ya yi kira ga gwamnan da ya sake duba jerin sunayen don kaucewa rikicin doka a nan gaba, cewar Daily Nigerian.

“Dukkan sunayen da aka bayar mambobin jam’iyya ne, za a so a ce NSIEC ta zama mai zaman kanta ba tare da son zuciya ba.
“Na tabbata idan an kalubalanci wannan a kotu, ba za a tabbatar da sahihancin jerin sunayen ba saboda rashin adalci.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

“Shawarata ita ce a sake duba lamarin domin kaucewa matsala, idan wani abu ya faru, kudaden kananan hukumomi za su shiga matsala kuma hakan zai iya shafar ayyukanka."

- Yahaya Mohammed-Usman

Dan jam’iyyar adawa ta PDP, Malami Abdullahi, ya ce gwamnan baya janye duk wani nadi da ya yi duk da kakkausan suka.

Ya bada misalin yadda kungiyar NLC ta yi Allah wadai da wasu nade-nade da gwamnan ya yi a baya saboda saba wa dokar aikin gwamnati.

Ramadan: Gwamna zai rage farashin abinci

Kun ji cewa gwamnatin jihar Niger za ta dauki matakin rage farashin kayan abinci domin saukaka wa jama’a a watan Ramadan da ake shirin shiga.

Gwamna Umaru Bago ya ce jihar ta girbi fiye da ton miliyan daya na masara, kuma ana amfani da kamfanin Niger Foods wajen daidaita farashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel