"An Zuba wa INEC Ido Ta na Sha'aninta," Makusancin Kwankwaso Ya Dira kan Hukumar Zabe
- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, ya ce dole ne a hukunta INEC da jami’an gwamnati kan kura-kuran zaɓe da ake maimaita wa
- Bishof Isaac Idahosa ya kuma ba hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa shawarar yadda za a kauce wa aikata magaudi a zabukan Najeriya
- A kan rikicin NNPP, makusancin na Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa babu wani tsagi a jam'iyyarsu, domin tuni aka kori masu son kawo rikici
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Bishof Isaac Idahosa, ya ce dole ne a hukunta hukumar zaɓe ta kasa (INEC).
Baya ga hukumar INEC, Bishof Idahosa na son a kara da hukunta jami'an gwamnati saboda kura-kuran da suka faru a zaɓe.

Asali: Facebook
A hirar da ya yi da Channels Televsion, tsohon ɗan takarar a karkashin NNPP, ya koka kan yadda ba a duba kura-kuran da INEC ke tafkawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba a hukunta hukumar INEC,” Idahosa
Bishof Idahosa ya bayyana cewa akwai kurakurai a yadda ake barin hukumar zaɓe ta INEC tana aikinta ba tare da kulawa ba.
Ya ce:
“Ba mu hukunta kowa a kan abin da ya aikata; babu hukunci, don haka ana ci gaba da maimaitawa.”
Ya ƙara da cewa:
“INEC na aikata kura-kurai, amma ba wanda ke sa ido a kanta, don haka su kan ci gaba da maimaita kurakuran.
Bishof Idahosa ya ba INEC shawara
Jagora a jam'iyyar NNPP ya bukaci a daidaita tsarin zaɓe ta yadda za a gudanar da duk zaɓukan a rana guda domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Ya ce:
“Ina son bayar da shawarar a gudanar da dukkan zaɓuka a rana guda. Wannan zai taimaka matuƙa wajen hana maguɗi – zaɓen shugaban ƙasa, sanata, da gwamna duk a rana guda. Zai rage kashe kuɗi kuma a samu sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan
Ana zargin gwamna ya ɗirkawa fitacciyar jaruma ciki a Najeriya, gaskiya ta bayyana
Amma idan an raba su mako ɗaya ko biyu bayan zaɓen shugaban ƙasa, ana iya yin maguɗi ko amfani da tasirin wani zaɓe a wani.”
‘Har yanzu ina kusa da Kwankwaso’ – Idahosa
Bishof Idahosa ya bayyana cewa har yanzu ya na da da kusanci da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma har yanzu shi ne jagora a NNPP.
Ya ce:
“Da farko, har yanzu ina kusa da shugabana. Ya zo nan makon da ya gabata – ranar 8 ga Fabrairu lokacin da nake bikin cikar shekaru 60.
Don haka har yanzu muna da kusanci, muna da kyakkyawar alaƙa. Babu wata matsala a jam’iyyarmu, har yanzu shi ne jagoranmu na ƙasa, Mai girma Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.”
“Ba mu da ɓangarori daban-daban; tuni an kore su daga jam’iyya. Babu wata bukata ta yayata maganar baraka a jam’iyyarmu – muna da jam’iyya guda da ke ƙarƙashin jagorancin Mai girma Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.”
Yadda Kwankwaso ya zabi Idahosa a 2023
A baya, mun wallafa cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ya yi bincike mai zurfi kafin ya zaɓi abokin takararsa.
A yayin kaddamar da Bishof Isaac Idahosa a matsayin mataimakin takararsa a babban zaɓen 2023, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya duba sama da mutane 20 kafin yanke shawara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng