Tsohon Shugaban PDP Ya Bi Sahun Ɗan Majalisa, Ya Tattara Jiga Jigai Sun Koma APC
- Jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas ta karɓi tsohon shugaban PDP da magoya bayansa da suka koma cikinta
- Barista Ufeanyi Nworie tare da wasu kusoshin PDP da ɗumbin magoya baya sun sauya sheka zuwa APC don ba da gudummuwa wajen kawo ci gaba
- A taron da aka shirya domin tarbarsu, shugaban APC ya buƙaci su ba Gwamna Nwifuru haɗin kai a ƙoƙarinsa na ɗaga darajar jihar Ebonyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi - Tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi, Barista Ifeanyi Nworie, tare da magoya bayansa, sun sauya sheka zuwa APC mai mulki.
An tarbi Barista Nworie a wani bikin karramawa da jam'iyyar APC ta shirya masa a karamar hukumar Ezza ta Kudu a jihar Ebonyi.

Asali: Getty Images
Shugaban APC na jihar Ebonyi, Chief Stanley Emegha, da wasu ƙusoshi ne suka karɓi masu sauya shekar hannu bibbiyu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Ana zargin gwamna ya ɗirkawa fitacciyar jaruma ciki a Najeriya, gaskiya ta bayyana
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta bukaci su ba gwamna haɗin kai
Da yake jawabi a taron, Emegha ya bukaci masu sauya sheƙar su ba Gwamna Francis Nwifuru cikakken goyon baya domin cimma burinsa na ɗaga ƙimar jihar.
Mista Emegha ya baygana cewa rikici da gaba a siyasa ba sa amfanar kowa, don haka ya nuna muhimmancin haɗa kai domin ci gaban al'ummar Ebonyi.
Ya ce sai da ya tuntubi dan takarar gwamna na PDP a 2023, Ifeanyi Chukwuma Odii, domin ya hada kai da Gwamna Nwifuru don ci gaban jihar.
Sannan ya bukaci shugabannin APC a Ezza ta Kudu da su karɓi sababbin ‘yan jam’iyyar hannu biyu-biyu tare da ba su cikakkiyar dama a cikin harkokinta.
Menene yake jawo mutane APC a Ebonyi?
A nata ɓangaren, shugabar karamar hukumar Ezza ta Kudu, Mrs. Euphemia Nwali, ta bayyana farin cikinta tare da maraba da masu sauya sheƙar.
Ta ƙara da cewa ci gaban da gwamnatin Nwifuru ke samu tun bayan hawanta kan mulki yana daɗa ja hankalin ‘yan hamayya su sauya sheka zuwa APC.
Shugabar ƙaramar hukumar ta tabbatar da cewa gwamnan zai ci gaba da tafiyar da gwamnatinsa a bude kuma kofarsa a buɗe take ga kowa.
Dalilin sauya shekar ƙusoshin PDP
A nasa jawabin a madadin masu sauya shekar, Barr. Nworie ya ce sun yanke shawarar komawa APC ne ba don rikicin da ke faruwa a PDP ba.
Ya sha alwashin hada kai da gwamnatin jihar karkashin Gwamna Nwifuru wajen kawo ci gaba ga al'umma.
Ya kuma jaddada cewa ba zai zama silar rarraba jam’iyyar ba, yana mai fatan ganin APC ta lashe dukkan kujerun shugabanci a zaben 2027.
APC ta samu ƙarin ɗan Majalisar wakilai
A wani labarin, kun ji cewa Hon. Garba Koko ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC a zauren Majalisar wakilan tarayta da ke Abuja ranar Laraba.
Ɗan Majalisar ya tabbatar da komawa APC ne a wata wasika da kakakin Majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya karanta ga sauran mambobi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng