Shaidar APC Ya ba Jam'iyya Kunya a Kotu, Ya Ce an Yi Magudi a Zaben Gwamna

Shaidar APC Ya ba Jam'iyya Kunya a Kotu, Ya Ce an Yi Magudi a Zaben Gwamna

  • Wani shaidar jam’iyyar APC, Afuda Theophilus, ya amince cewa an samu kuri’u fiye da adadin masu kada kuri’a a zaben gwamnan Edo
  • Shaidar da aka gabatar domin kare sahihancin zaben ya shaida cewa hukumar INEC ta gaza cikawa takardun da suka dace kafin kada kuri’a
  • Wannan bayanin ya jefa shakku a kan sahihancin sakamakon zaben, wanda ka iya yin tasiri ga hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Shari’ar zaben gwamnan jihar Edo ta dauki sabon salo yayin da shaidar jam’iyyar APC, Afuda Theophilus, ya amince cewa an samu kuri’u fiye da yawan masu kada kuri’a.

Afuda Theophilus ya ce an samu aringizon kuri'un ne a karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabashin jihar.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya ƙara bayyana da musulmi suka fara shirye shiryen azumin watan Ramadan

Zaben Edo
Shaidar APC ya ce an tafka kurakurai a zaben Edo. Hoto: Hoto: Adamu Ogie Shaka/Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa Theophilus da aka gabatar domin kare sahihancin zaben, ya fara da cewa babu magudi a cikinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai yayin amsa tambayoyi daga lauyan bangaren adawa, Abiodun Owonikoko (SAN), ya amince cewa sakamakon kada kuri’a ya wuce yawan masu rijista a wasu rumfunan zabe.

Lamarin ya haifar da tambayoyi masu yawa kan yadda hukumar INEC ta gudanar da zaben, musamman kan rashin cika wasu takardun da doka ta shimfida.

Zaben Edo: Shaidar APC ya ce an yi kuskure

A yayin shari’ar, an tambayi Theophilus ko yana sane da sahihancin takardar da ake amfani da ita wajen rubuta lambobin sirrin kayan zabe kafin kada kuri’a.

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a karon farko, ya amince da hakan, amma daga bisani ya nuna shakku.

A lokacin da aka nuna masa takardun da aka yi amfani da su a ranar zabe, sai ya amince da cewa babu lambobi, sa hannun jami’an zabe ko wata alama da ke nuna cewa an cike takardun.

Kara karanta wannan

Mummunar rigima ta kaure tsakanin ƙungiyoyi 2 kan 'kuɗi', an kashe mutane sama da 10

Lauyan bangaren adawa, Owonikoko, ya tambaye shi:

"Za ka iya tabbatar da cewa babu lambobin sirri na sakamakon zabe ko na’urar BVAS a kan takardun?"

Theophilus ya amsa da cewa:

"Ba zan iya ganin su ba..."

Da aka matsa masa da tambayoyi, sai ya amsa:

"Eh, babu su a wurin."

Amsar ta kara jefa shakku kan yadda hukumar INEC ta gudanar da zaben, tare da nuna zargin cewa ba a bi ka’idojin zabe yadda ya kamata ba.

Martanin 'yan adawa a kan shari'ar

Rahotanni sun nuna cewa bayanin Theophilus ya ba bangaren adawa damar karfafa hujjarsu a gaban kotu.

Ogbeide Ifaluyi-Isibor, wanda ya yi magana a madadin bangaren adawa, ya ce gazawar cike takardun kadai ya isa a ce ba a bi dokokin zabe ba.

Ya ce:

"Doka ce, ba ra’ayi na ba ne. Hakan yana nufin ba a bi dokokin zabe ba. Muna godiya ga APC da ta turo mana shaidar da ke bayyanawa duniya gaskiya."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta fusata, an ba da umarnin farauto makasan malamin addini

Martani ya kara nuna cewa shari’ar na iya zama barazana ga sakamakon zaben, musamman ganin cewa shaidar da aka kira domin kare APC ne ke tabbatar da kura-kurai.

Shugaban APC ya yi magana kan 2027

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan makomar siyasar 2027.

Abdullahi Ganduje ya ce ya kamata 'yan Arewa su hakura da shugabancin Najeriya har sai Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa'adi na biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng