Siyasar Kano Ta Rikice: Kusoshin NNPP Sun Watsar da Kwankwaso, Sun Kama Layin APC

Siyasar Kano Ta Rikice: Kusoshin NNPP Sun Watsar da Kwankwaso, Sun Kama Layin APC

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karbi dandazon 'yan NNPP da suka sauya sheka zuwa APC
  • Wasu daga cikin wadanda suka sauya shekar sun ce sun gaji da salon jagorancin gidan Kwankwasiyya mai kama da kama karya
  • Sanata Barau ya yi ikirarin cewa yanzu tasirin NNPP ya ragu sosai a Kano kuma manyan ‘yan siyasar jihar na ta ficewa zuwa APC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karbi ƙungiyoyi uku na shugabannin NNPP da suka koma jam’iyyar APC.

Alhaji Abdullahi Sani Kwami, tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano, ya jagoranci rukunin farko na masu sauya shekar.

Sanata Barau ya yi magana da ya karbi shugabannin NNPP da suka sauya sheka zuwa APC
Wasu kusoshin NNPP a Kano sun sauya sheka zuwa APC ta hannun Sanata Barau Jibrin. Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

Sanata Barau ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X mai taken: 'An samu karin shugabannin NNPP da suka shiga APC.'

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban PDP ya bi sahun ɗan Majalisa, ya tattara jiga jigai sun koma APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kusoshin NNPP sun sauya sheka zuwa NNPP

Sanarwar ta ce Alhaji Kwami, wanda aka fi sani da 'dala', ya jagoranci shugabannin NNPP daga matakin gunduma da shugabannin mata zuwa APC ta hannun Sanata Barau.

A hannu guda, wasu tsofaffin shugabannin ɗalibai ƙarƙashin jagorancin Mohammed Nafiu Danlami, sun jefar da hulunnan Kwankwasiyya don rungumar APC.

Sun ce sun fice daga jam'iyyar ne saboda salon jagorancin NNPP mai kama da kama-karya da kuma manufofin Kwankwasiyya da ba su amfanar talakawa, inji Sanata Barau.

'NNPP ta rage tasiri a Kano' - Sanata Barau

Haka nan, Sanata Barau ya sanar da cewa Abba Kafi Gwamna, fitaccen jagoran matasa na NNPP a garin Getso da ke Gwarzo, ya jagoranci mabiyansa zuwa APC.

Sanarwar ta ce Abba ya bayyana cewa ayyukan raya ƙasa da tsare-tsaren Sanata Barau ne suka jawo su cikin jam'iyyar APC.

Yayin maraba da su, Sanata Barau ya taya su murna bisa ficewa daga "ƙaramar jam’iyya da ba ta da tasiri sai a wasu 'yan tsirarun gundumomi na kwaryar Kano."

Kara karanta wannan

'Najeriya ta rasa aboki': An shiga jimami da tsohon shugaban kasa ya kwanta dama

A cewarsa, jam'iyyar NNPP ba ta da tasiri a Kano ta Arewa, yayin da manyan ‘yan siyasa a Kano ta Kudu ke shirin barin ta zuwa APC.

Kalli hotunan wadanda suka sauya shekar a kasa:

'Yan siyasar da za su iya ba Abba matsala a 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana hasashen Gwamna Abba Yusuf zai nemi tazarce a 2027, inda zai kara da 'yan adawa musamman daga APC.

Sanata Barau Jibrin, Nasiru Gawuna, na cikin 'yan siyasa biyar da ake ganin za su iya ba Gwamna Abba matsala a neman tazarcensa a 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.