Wuyan Tsohon Minista Ya Yi Kauri, Ya Magantu kan Neman Takarar Shugaban Kasa

Wuyan Tsohon Minista Ya Yi Kauri, Ya Magantu kan Neman Takarar Shugaban Kasa

  • Shugaban bankin raya Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina da ke shirin barin mukamin, ya bayyana cewa yana da sha’awar takarar shugaban ƙasa
  • A cikin wata hira, Akinwumi Adesina ya bayyana cewa yana shirye ya yi hidima ga ƙasa, Afirka, ko duniya gaba ɗaya, ciki har da Najeriya
  • Dakta Adesina ya ce burinsa shi ne ganin rayuwar mutane na sauyawa, ya kuma ambaci cewa yana alfahari da kasancewarsa ɗan kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban bankin raya Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina ya magantu kan takarar shugaban kasa.

Dakta Akin Adesina da ke shirin kammala wa'adinsa ya yi nuni da yiwuwar yin takarar shugaban kasa a nan gaba.

Tsohon minista ya yi magana kan neman takarar shugaban kasa
Tsohon minista, Akinwumi Adesina ya nuna sha'awar neman takarar shugaban kasa a nan gaba. Hoto: Akinwumi Adesina.
Asali: Facebook

Adesina ya magantu kan yiwuwar takara shugaban kasa

Adesina, wanda tsohon ministan noma ne a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya bayyana hakan a wata hira da Rufai Oseni na Arise TV.

Kara karanta wannan

'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban AfDB ya bayyana cewa yana shirin yin hidima ta ƙasa bayan kammala aikinsa a bankin.

“Zan kasance a shirye in yi hidima a kowane matsayi, a duniya, a Afirka, ko a Najeriya.”

- Akinwumi Adesina

Babban abin da ya fi farantawa Adesina rai

Adesina ya ce abu mafi faranta masa rai shi ne ganin yadda rayuwar mutane ke sauyawa da cigaba, cewar TheCable.

Da aka tambaye shi menene makomarsa da kuma ko yana shirin yin takarar shugabancin Najeriya, sai ya ce:

“Ka san, ɗaya daga cikin abubuwan da nake alfahari da su a matsayina na ɗan Najeriya, shekaru da yawa da suka wuce, na samu damar samun bizar Amurka.
"An ba ni biza, kuma zan iya samun zama ɗan ƙasar Amurka, amma na ce, ba na buƙata, ba wai don ba na son Amurka ba.
“Allah bai yi kuskure ba wajen halitta ni a matsayin ɗan Afirka, Zan rayu a matsayin ɗan Najeriya, kuma zan yi tafiya da yardar Allah.

Kara karanta wannan

Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA

“Ka duba, abu guda da ke faranta mani rai ba komai ba ne illa ganin rayuwar mutane na inganta da canzawa shi ne ke ba ni gamsuwa.
"Saboda haka, a sakamakon hakan, zan kasance a shirye in yi hidima a kowane matsayi, a duniya, a Afirka, ko a ƙasata, Najeriya.

Jaridar This Day ta kawo rahoton hirar da aka yi da masanin aiki gonan a yammacin Litinin.

Adesina zai marawa Bola Tinubu a baya

A wani labarin, shugaban bankin raya kasashen Afrika, AfDB, Akinwumi Adesina, ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a taron koli na kudi na duniya.

Adesina ya ce shugaban kasa Tinubu wanda ya karbi mulki a watan Mayun 2023 ya burge shi da kyawawan manufofinsa kan tattalin arzikin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel