Ba a samu Dr. Akinwumi Adesina da laifi ba bayan an duba binciken bankin AfDB

Ba a samu Dr. Akinwumi Adesina da laifi ba bayan an duba binciken bankin AfDB

- An wanke shugaban bankin AfDB, Dr. Akinwumi Adesina daga zargi

- Kwamitin bincike bai samu shugaban bankin cigaban Afrikan da wani laifi ba

- Tsohuwar shugabar kasar Ireland, Mary Robinson ce ta jagoranci wannan bincike

Shugaban babban bankin cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina ya fito kal a binciken da aka yi bayan an zarge shi da aikata ba daidai ba a AfDB.

A ranar 28 ga watan Yuli, mu ka samu labari daga jaridar BuinessDay cewa kwamitin da ya binciki Akinwumi Adesina, bai same shi da laifi ba.

Wani kwamiti na musamman da aka kafa ne ya gudanar da bincike, ya kuma fitar da rahoto jiya bayan ya saurari Akinwumi Adesina da korafin da ke kansa.

Tsohuwar shugabar kasar Ireland, Mary Robinson mai shekaru 76 ce ta jagoranci wannan kwamiti na mutum uku da ya yi wani bincike na musamman.

KU KARANTA: Buhari ya sa labule da shugaban-bankin AfDB

Ba a samu Dr. Akinwumi Adesina da laifi ba bayan an duba binciken bankin AfDB
Akinwumi Adesina Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Kafin yanzu wani kwamiti ya binciki Dr. Adesina, kuma bai same shi da aikata laifin da ake zarginsa da su na rashin gaskiya da badakala ba.

Duk da haka kasar Amurka ta huro wuta a kan cewa dole sai an duba aikin da tsohon ministan harkar gonan Najeriyar ya ke yi a ofis.

A dalilin haka aka ba Robinson wanda ta yi mulki tsakanin 1990 da 1997 alhakin binciken shugaban na AfDB, ita ma ta kammala aiki ba tare da ta gano wata barna ba.

Aikin kwamitin Mary Robinson shi ne duba binciken da aka yi a baya, ba wai ta kirkiro sabon zargi ba. A karshe an tabbatar da ingancin aikin kwamitin bankin.

Ministan kudin kasar Amurka, Steven Mnuchin, ya sha ban-ban da shugabannin da ke sa ido a kan aikin AfDB, ya fito ya na kira a binciki Adesina na musamman.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel