Matakin da APC Ta Dauka kan 'Ya'yanta da Suka Bauɗe, Suke Cin Mutuncin Tinubu, Ganduje
- Shugabannin APC a Arewa ta Tsakiya sun gargadi ‘ya’yansu su daina cin mutuncin Bola Tinubu da sauran jiga-jigan jam’iyyar a kafofin watsa labarai
- A wata sanarwa, shugabannin yankin sun ce ba za su amince da bata suna ba, kuma za su dauki mataki kan duk masu tada zaune tsaye
- Jam’iyyar ta jaddada goyon bayanta ga shugabanninta, tana mai cewa duk wani kokari na ci musu mutunci zai gamu da hukunci mai tsanani
- Daga cikin wadanda ake lissafo da ake gargadin mutane da cin mutuncinsu akwai Abdullahi Ganduje da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ta gargadi wasu ‘ya’yanta da kungiyoyin goyon baya da ke zagin Bola Tinubu da sauran shugabannin jam’iyya.
Jam'iyyar ta kuma gargadi masu cin mutuncin Shugaban APC, Dr Abdullahi Ganduje da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume a kafofin sadarwa

Asali: Twitter
APC ta gargadi masu sukar Tinubu, Ganduje.
Wannan gargadi na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar 8 ga watan Janairun 2025 a Abuja, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar wacce Shugaban APC na Arewa ta Tsakiya, Mu’azu Rijau, da Sakataren yankin, Yakubu Adamu, suka sanyawa hannu sun koka kan lamarin.
A yan kwanakin nan, Akume shima ya fuskanci suka mai tsanani saboda sabaninsa da Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, Tribune ta ruwaito.
Yayin da yake bayani, Rijau ya ce shugabannin jam’iyyar ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya saba dokokin jam’iyya.
Ya bayyana cewa an yanke hukuncin daukar mataki a wata muhimmiyar ganawa da shugabannin jam'iyyar APC na yankin da shugabannin jihohi a Abuja.
Matakin da APC za ta dauka kan wasu 'ya'yanta
Sanarwar ta ce:
“Shugabancin APC na Arewa ta Tsakiya sun fusata da yadda wasu mutane da kungiyoyi ke amfani da sunan jam’iyya suna cin mutuncin wasu manyan shugabanninmu a kafafen watsa labarai.

Kara karanta wannan
'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu
"Mun fi mayar da hankali kan hare-haren da ake kaiwa tsohon gwamnan Jihar Benue kuma SGF na yanzu, Sanata George Akume, daga wasu kungiyoyin da aka dauki haya.
“Shugabannin jam’iyyar a yankin suna goyon bayan shugabanninsu, musamman Akume da gwamnonin APC guda biyar da ke yankin.
“Muna gargadin wadannan mutane da kungiyoyi su daina cin mutunci da zagin shugabanninmu, idan ba haka ba, za su fuskanci hukunci mai tsanani.”
Tinubu ya tura sako ga yan adawa
Kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta yi watsi da shirin da wasu ‘yan adawa suke yi, tana mai cewa Shugaba Tinubu bai damu ba kuma ko a jikinsa.
Hadimin shugaban, Sunday Dare ya bayyana taron a matsayin shiri na cin mutunci da fitar da kalamai masu tayar da zaune tsaye.
Asali: Legit.ng