Buhari Ya Ajiye Girma Ya Yi Jinjina ga Wanda Ya Taimaka Masa Sosai a 2015

Buhari Ya Ajiye Girma Ya Yi Jinjina ga Wanda Ya Taimaka Masa Sosai a 2015

  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jinjinawa tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, yayin da ya cika shekara 60 a duniya
  • Buhari ya ce Fayemi babban jigo ne da ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC tare da kawo sauyi a siyasar Najeriya
  • Ya kuma yaba da irin kishin kasa da biyayya ga jam’iyya da Fayemi ya nuna, yana mai addu’a Allah ya kara masa lafiya da tsawon rai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yabawa tsohon gwamnan jihar Ekiti, John Kayode Fayemi, yayin da ya ke bikin cikarsa shekara 60 a duniya.

Buhari ya bayyana Fayemi a matsayin jagora nagari da ya taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, musamman wajen hadewar jam’iyyun adawa da kuma tabbatar da dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

2027: Kashim Shettima ya fadi yadda ya ke mu'amalantar Atiku a bayan fage

Buhari
Buhari ya yabawa tsohon gwamnan jihar Ekiti bayan cika shekaru 60. Hoto: Garba Shehu|Kayode Fayemi
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, Buhari ya ce Fayemi ya cancanci yabo saboda sadaukar da kansa wajen cigaban kasa da kuma irin hangen nesa da ke tattare da shugabancinsa.

Buhari: 'Fayemi jigo ne a siyasar Najeriya;

Muhammadu Buhari ya ce Kayode Fayemi na daya daga cikin manyan mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC.

Ya tuna da yadda Fayemi ya taka rawar gani a 2015, lokacin da APC ta hambarar da gwamnatin PDP, wanda ya bai wa Buhari damar zama shugaban kasa.

Buhari ya ce rawar da Fayemi ya taka a matsayin daraktan yakin neman zabensa, da kuma gwagwarmayar dimokuradiyya da ya yi za su ci gaba da kasancewa tarihi a siyasar Najeriya.

Ya ce kishin kasa da jajircewar Fayemi wajen ganin an kafa gwamnati mai inganci sun kara masa daraja a idon jama’a.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Tinubu ya bayyana babban abin da ya saka a gaba a Najeriya

Fayemi ya nuna dattaku inji Buhari

Shugaba Buhari ya jinjinawa Fayemi saboda yadda bai nuna fushi ba lokacin da ya fadi zaben gwamna a 2014.

Ya ce duk da yadda wasu ‘yan jam’iyyarsa suka juya masa baya, bai dauki abun da zafi ba, maimakon haka sai ya sake shirya kansa har ya sake lashe zabe a 2018.

Tsohon shugaban kasar ya ce wannan baiwa ta hakuri da jajircewa ita ce ta bambanta Fayemi da sauran shugabanni.

Ya ce kowa ya shaida irin namijin kokarin da Fayemi ya yi a wa’adinsa na biyu domin ci gaban jihar Ekiti.

Buhari ya yi wa Fayemi fatan alheri

Buhari ya bayyana farin cikinsa da kasancewarsa tare da Fayemi a matsayin abokin siyasa da kuma shugaba mai biyayya.

Ya ce yana alfahari da irin gudunmawar da Fayemi ya bayar a matsayin minista da kuma gwamna a mulkinsa.

Kara karanta wannan

'Na bambanta da su': Buhari ya fadi halin da abokansa na yarinta da karatu ke ciki

A karshe, Buhari ya yi wa Fayemi fatan alheri da addu’ar Allah ya kara masa lafiya da tsawon rai domin cigaba da hidimtawa Najeriya.

Ya taya Fayemi murnar zagayowar ranar haihuwarsa, yana mai addu’ar Allah ya raya shi cikin lafiya da albarka.

Kwamishinan Ganduje ya koma NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Rabi'u Musa Kwankwaso ya karbi tsohon Kwamishinan Abdullahi Ganduje da ya sauya sheka.

Rahoton Legit ya nuna cewa Sanata Rabi'u Kwankwaso ya karbi Barista Falali ne zuwa jam'iyyar NNPP a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng