Hukumar INEC Ta Gaza Tabbatar da Nasarar Gwamna a Kotu, Alkali Ya Ɗauki Mataki
- Hukumar zaɓe watau INEC ta gaza gabatar da ko shaida ɗaya da zai tabbatar da sahihancin sakamakon zaben gwamnan jihar Edo
- A zaman yau Alhamis, lauyan INEC ya shaida wa kotu cewa hukumar ta canza shawara, yana mai cewa babu bukatar gabatar da shaida
- Alkalin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamnan ya ɗage zaman zuwa ranar Litinin, 10 ga watan Fabrairu, 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gaza gabatar da shaidun kamar yadda ta yi alƙawari a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan Edo.
A zaman kotun na ranar Alhamis, INEC ba ta kawo shaida ko ɗaya da za ta kare ayyana dan takarar APC, Monday Okpebholo, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Edo da aka gudanar a ranar 21 ga Satumba, 2024 ba.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu, an kori kwamishinoni 3 daga aikin INEC

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta tattaro cewa tawagar lauyoyin INEC ƙarƙashin Kanu Agabi (SAN) ta shaidawa kotun cewa babu bukatar gabatar da shaida a shari'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
INEC ta gaza gabatar da shaida a kotu
Wannan mataki ya zo ne kasa da awa 24 bayan INEC ta shaida wa kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Wilfred Kpochi cewa tana da shaidu guda biyar.
A cewar hukumar zaɓen, shaidun da za ta gabatar za su tabbatar da sahihancin sakamakon da ta bayyana wanda Gwamna Okpebholo ya samu nasara.
A baya, INEC ta nemi kotun da ta dage shari’ar zuwa ranar Alhamis, tana mai cewa shaidun da take da su za su zo daga Birnin Benin, Edo State.
Hukumar INEC fa fasa gabatar da shaidu
A zaman kotun a Abuja, lauyan INEC, Agabi (SAN), ya ce bayan sun bar kotun a ranar Laraba, sun sake nazarin lamarin kuma suka yanke shawarar cewa “abin da ya fi dacewa shi ne a rufe shari’ar wanda ake ƙara na farko (INEC)."

Kara karanta wannan
Gwamna ya gano badaƙalar kudi, ya dakatar da kwamishina da shugaban hukuma nan take
A nasu ɓangaren, jam’iyyar PDP da dan takararta, Asue Ighodalo, sun bayyana cewa ba su yi mamaki da wannan mataki ba, kamar yadda Punch ta kawo.
Lauyan masu ƙarar, Adetunji Oyeyipo, ya ce:
“Gaskiya ne, ba mu yi mamaki ba, kuma wannan dama ce da wanda ake ƙara na farko ke da ita. Ba mu da wata jayayya a kai."
Alkalin kotun ya ɗauki mataki na gaba
Bayan INEC ta gaba gabatar da shaidu, lauyoyin Gwamna Okpebholo da SPC, Onyechi Ikpeazu da D. C. Dewigwe sun roƙi kotun da ta ba su lokaci domin tattara shaidunsu kuma su fara kare kansu.
A sakamakon haka, kotun ta ɗage zaman shari’ar zuwa ranar Litinin, domin bai wa Gwamna Okpebholo damar buɗe karewarsa kan ƙarar da ke gabanta.
Ighodalo ya maka shugaban APC a kotu
A wani rahoton, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan Edo a inuwar PDP, Asue Ighoɗalo ya kai ƙarar shugaban APC na jihar gaban kotu a Legas.

Kara karanta wannan
"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura
Dr. Ighodalo ya nemi shugaban APC na jihar Edo, Jarret Tenebe ya biya shi diyyar Naira miliyan 500 na ɓata masa suna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng