"Waye Sakataren PDP?" Barau Jibrin Ya Zaƙalƙale da Hatsaniya Ta Ɓarƙe a Majalisar Dattawa

"Waye Sakataren PDP?" Barau Jibrin Ya Zaƙalƙale da Hatsaniya Ta Ɓarƙe a Majalisar Dattawa

  • Sanata Barau Jibrin ya ƙalubalanci sanatocin PDP yayin da taƙaddama ta barke a Majalisar dattawa kan sauya shekar Sanata Ned Nwoko
  • Bayan sanar da komawar Nwoko APC, Sanata Abbba Moro ya ƙaryata cewa PDP ta rabu gida biyu, lamarin da ya tayar da hayaniya a Majalisar
  • Mataimakin shugaban Majalisar dattawa da shugaban masu rinjaye sun yi wa Abba Moro ruwan martani a jiya Laraba da ake surutun

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - An yi hayaniya da musayar yawu mai zafi a zauren Majalisar Dattawa yayin da Sanata Ned Nwoko (Delta ta Arewa) ya fice daga PDP zuwa APC.

Mataimakin shugaban Majalisar, Barau Jibrin da shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele sun yi ka-ce-na-ce da shugaban marasa rinjaye, Abba Moro.

Majalisar dattawa.
An yi musayar yawu a Majalisar dattawa kan sauya shekar Sanata Ned Nwoko Hoto: @mob_sen_leader
Source: Twitter

Sanata Nwoko ya faɗi dalilin ficewa daga PDP

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa hatsaniyar ta ɓarke ne da Sanata Nwoko ya bayyana cewa ya yanke barin PDP ne saboda rigingimun da ke addabar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi jihar da suka shirya kwatowa, ya lissafa nasarorin Tinubu

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar sauya shekar Sanata Nwoko, wanda ya roki a kafa kwamitin da zai bincike halin da PDP ke ciki.

A cikin wasikar mai taken "Sanarwar ficewa daga PDP zuwa APC," Nwoko ya bayyana cewa rikicin ya raunata PDP kuma ya hana ta zama ingantacciyar jam’iyyar adawa.

Ya gargaɗi cewa wannan rikici barazana ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya, yana kwatanta shi da 'batun gaggawa na ƙasa' wanda ya dace a ɗauki matakin magance shi.

An nemi Majalisa ta sa baki a rikicin PDP

Ned Nwoko ya ce gaza magance matsalar na iya haifar da tsarin jam’iyya guda ɗaya, wanda hakan zai zama hatsari ga tafiyar da mulki da kuma zaman lafiyar ƙasa.

Nwoko ya bukaci Majalisar Dattawa da ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki rikicin cikin gida da PDP ke fuskanta tare da ba da shawarwari kan yadda za a kare tsarin jam’iyyu da yawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba sakataren APC a Kano Babban muƙami bayan minista ya bar kujerar

Sai dai jim kaɗan bayan da Akpabio ya karanta wasikar, Sanata Moro ya miƙa ƙorafi bisa tanadin doka, inda ya karyata ikirarin da Nwoko ya yi.

Yadda hatsaniya ta ɓarke a Majalisar dattawa

Da yake ambato sashe na 68(g) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, Abba Moro ya jaddada cewa PDP ba ta rabu kashi biyu ba, don haka sauya sheƙar Nwoko ya saba doka.

Amma Barau ya ƙalubalanci wannan batu, yana mai cewa PDP ta rabu kashi biyu, ya ambaci tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi.

Sanata Barau Jibrin ya kuma tambayi Abba Moro da ya bayyana wa majalisa waye sahihin sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa, tambayar da ya gaza amsawa.

"Wannan sauya sheƙa kamar girgizar ƙasa ce, kuma za ta jawo wasu sanatoci da dama su fice daga PDP," in ji Barau.

A nasa martanin, Sanata Bamidele ya soki kalaman Abba Moro, yana mai cewa sashen kundin tsarin mulkin da ya ambata a zahiri yana kare sauya sheƙar Nwoko, duba da irin rabuwar da ke cikin PDP.

Kara karanta wannan

"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura

Tinubu ya aika saƙo Majalisar dattawa

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattatwa ta amince da ƙara kasafin kudin 2025 daga N49.7trn zuwa N54.2trn.

Buƙatar shugaban ƙasar na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan Majalisar ta dawo daga hutun ƙarshen shekara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262