An Tasa Keyar Farfesa Gidan Kaso, Ana Zargin Wani da Taimakawa Akpabio a Zabe
- Wata kotu a Uyo ta yanke hukuncin daurin shekaru uku ga Farfesa Ignatius Uduk kan laifin karya da wallafa sakamakon zaben bogi a 2019
- Alkalin kotu ya ce hujjojin da masu shigar da kara suka gabatar sun tabbatar da cewa Farfesa Uduk ya aikata laifin da aka tuhume shi da shi
- Hukuncin ya biyo bayan shari'ar wani Farfesa, Peter Ogban, wanda aka daure shi shekaru uku a gidan yari kan laifin kwaskwarimar sakamakon zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Uyo, Akwa Ibom - Wata Babbar Kotun Jiha a Uyo, Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa wani Farfesa dan Najeriya hukuncin daurin shekaru uku a gidan kaso.
Ana zargin Farfesa Ignatius Uduk da laifin karya da wallafa sakamakon zabe na bogi a zaben da aka gudanar a 2019.

Asali: Original
An daure Farfesa kan taimakawa Akpabio a zabe

Kara karanta wannan
Tinubu ya bukaci korar kwamishinonin zabe a jihohi 3 kan zargin rashin da'a a 2023
Channels TV ta ce Farfesa Uduk, malami ne a Jami’ar Uyo da hukumar INEC ce ta gurfanar da shi bisa tuhumar aikata laifuka a Mazabar Essien Udim.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncinsa yana zuwa ne shekaru hudu bayan wani Farfesa Peter Ogban, wanda shi ma aka daure shi shekaru uku.
Ana zargin Ogban bisa laifin kwaskwarimar sakamakon zabe don taimakawa Godswill Akpabio wanda yanzu shi ne shugaban majalisa.
A 2019, Farfesa Ogban ya kasance jami’in tattara sakamakon zabe na INEC a zaben Sanatan Akwa Ibom Arewa ta Yamma, inda Akpabio ya sha kaye.
Akpabio ya yi takara ne a karkashin jam’iyyar APC, amma an same shi da laifin murde sakamako, cewar Premium Times.
Tsohon kwamishinan zabe na INEC a Akwa Ibom, Mike Igini, ne ya shigar da kara a kan Farfesa Ogban kuma ya tabbatar da cewa an daure shi kafin ya yi ritaya a 2022.
Kotu ta daure Farfesa na tsawon shekaru 3
A watan Disamba 2020 aka fara gurfanar da Farfesa Uduk bayan an bada umarnin kama shi saboda kin bayyana a kotu domin fara shari’a.
Farfesan ya musanta tuhume-tuhumen da hukumar INEC ta yi masa, amma shari’ar ta samu jinkiri saboda canza lauyan kare shi da kuma matsalolin lafiya.
An shirya yanke hukunci a ranar 29 ga Janairun 2025 amma aka daga zuwa 5 ga Fabrairu bayan wanda ake tuhuma da lauyansa sun gaza bayyana a kotu.
Alkali Bassey Nkanang ya soke belinsa kuma ya bada umarnin a sake kama shi, kafin daga baya aka kawo shi kotu a cikin keken guragu.
Da yake yanke hukunci, alkalin ya ce masu shigar da kara sun tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya wallafa sakamakon zabe na bogi a matsayin jami’in tattara sakamako.
Saboda haka, ya yanke masa hukuncin daurin shekaru uku kan kowanne daga cikin laifukan biyu, amma za a gudanar da hukuncin a lokaci guda.

Kara karanta wannan
Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya
An tura basarake gidan gyaran hali
Kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa dakataccen sarkin Orile Ifo a jihar Ogun wanda ake tuhuma da cin zarfi ya gaza cika sharuɗɗan beli.
Jami'an tsaro sun tasa keyar basaraken, Oba Abdulsemiu Ogunjobi zuwa gidan gyaran halin Ilaro domin ajiye shi zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng