"Me Suke Shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar Ya Kai Wa Sanata Binani Ta Bar Baya da Ƙura

"Me Suke Shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar Ya Kai Wa Sanata Binani Ta Bar Baya da Ƙura

  • An fara surutu da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya kai ziyara gidan Sanata Aishatu Binani a birnin Abuja
  • Wannan ziyara dai ta haifar da ce-ce-ku-ce da hasashen abin da ya kai Atiku gidan ƴar takarar APC a zaben gwamnan Adamawa a 2023
  • Wani na kusa da Atiku da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ziyarar ta zumunci cewa kawai amma tana da ma'ana a siyasar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyara gidan Sanata Aishatu Dahiru Binani da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata.

Wannan ziyara da Atiku ya kai wa ƴan takarar gwamnan Adamawa a inuwar PDP a 2023 ta janyo cece-kuce kan yiwuwar za su haɗa kai don tunkarar zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi jihar da suka shirya kwatowa, ya lissafa nasarorin Tinubu

Atiku da Aishatu Binani.
An fara surutu kan ganawar Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar da Aishatu Binani a Abuja Hoto: @IU_Wakili
Source: Twitter

Daily Trust ta ce ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da manyan jiga-jigan adawa ke ƙoƙarin kafa wata sabuwar gamayya domin kifar da gwamnatin APC a zaɓe mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da Aishatu Binani ke ciki a APC

Sanata Binani, jigo a APC na fuskantar barazana a siyasa bayan da babban abokin hamayyarta, Malam Nuhu Ribadu, ya samu muƙamin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (NSA).

Wannan ya sa ake hasashen cewa tana shirin sake tsayawa takara a 2027 domin kokarin zama mace ta farko da za ta zama gwamna a Najeriya.

A zaɓen 2023, Binani ta samu ƙuri’u 398,788, yayin da gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri na PDP ya lashe zaɓen da ƙuri'i 430,861 bayan kammala tattara kuri'u.

Menene dalilin ganawar Atiku da Binani?

Ko da yake Atiku da Binani ba su yi magana da manema labarai ba bayan ganawar da suka yi ba, amma hotunan ziyarar sun bazu a shafukan sada zumunta ranar Talata.

Kara karanta wannan

A hukumance, jam'iyyar APC ta samu ƙarin sanata 1 a Majalisar Dattawan Najeriya

Wani na kusa da Atiku ya bayyana cewa wannan ziyara “ziyara ce ta sada zumunta kawai,” amma ya yarda da cewa tana da babbar ma’ana a siyasa.

"Duk da cewa ana kokarin ɓoye lamarin, dangantakar Atiku da Gwamna Fintiri ta lalace kuma da alama ba za a iya gyara ta ba," in ji shi.

Mutane sun yi magana kan ziyarar Atiku

Wani mai amfani da shafin X (Twitter) mai suna Abdul-Aziz Na’ibi Abubakar ya rubuta cewa:

"Siyasa ba ta rago ba ce, kuna ganin Atiku Abubakar zai zama gadar da za ta kai Binani ga cimma burinta a 2027?"

Wani kuma, Abubakar H. Kapo, ya yi hasashen cewa:

"Idan aka samu haɗin gwiwa tsakanin Waziri Adamawa (Atiku), Sanata Binani, Sanata Nyako, Sanata Abbo da Dr. Modibbo Baba, wannan zai kasance gagarumin ƙalubale ga APC a Adamawa.
"Wannan tawagar idan suka haɗe wuri ɗaya, zaɓen 2027 a jihar Adamawa zai kasance mai kayatarwa sosai."

A halin yanzu, ana ci gaba da sa ido kan yuwuwar haɗin gwiwar Atiku da Binani da kuma tasirin hakan a siyasar Adamawa da ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Majalisar amintattun PDP ta shiga taron gaggawa a Abuja

APC ta fara kokarin kashe wutar rikicinta

Kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta fara ƙoƙarin rarrashi da haɗa kan ƴaƴanta domin tunkarar babban zaɓen 2027 da murya ɗaya.

Wasu manyan ƙusoshin APC sun gana a Adamawa domin duba abubuwan da ke damunsu da kuma lalubo hanyoyin da za a samu masalaha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262