"Gwamna da Abokin Takarar Atiku na Roƙon a Bari Su Shigo APC," Sanata Ya Ce Babu Wurinsu

"Gwamna da Abokin Takarar Atiku na Roƙon a Bari Su Shigo APC," Sanata Ya Ce Babu Wurinsu

  • Ɗan takarar gwamnan Delta a zaben 2023, Ovie Omo-Agege ya yi ikirarin Sheriff Oborevwori da Ifeanyi Okowa sun fara roƙon a bari su shigo APC
  • Sanata Omo-Agege, tsohon shugaban majalisar dattawa ya ce APC ba ta buƙatar gwamnan Delta da magabacinsa, Sanata Ifeanyi Okowa su dawo cikinta
  • Ya buƙaci ƴan APC a jihar Delta su kwantar da hankulansu kan rikicin cikin gidan da ke faruwa, ya ce jam'iyyar PDP ba za ta kai labari ba a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Sanata Ovie Omo-Agege ya yi ikirarin cewa Gwamna Sheriff Oborevwori da magabacinsa kuma abokin takarar Atiku Abubakar a 2023, Ifeanyi Okowa suna son shigowa APC.

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya buƙaci gwamnan Delta da Ifeanyi Okowa su yi zamansu a PDP domin ba su da wuri a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

2027: Masari ya taso masu son kawar da Tinubu a gaba, ya fadi makomarsu

Omo Agege da Gwamnan Delta.
Sanata Omo Agege ya yi ikirarin gwamnan Delta na son dawowa APC Hoto: Ovie Omo-Agege, Sheriff Oborevwori
Asali: Twitter

Omo-Agege, wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin APC a zaɓen 2023, ya bayyana cewa jam’iyya tana ƙara samun ƙarfi a jihar Delta, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ragowar Sanatan PDP na hanyar shiga APC

Ya ce ɗan majalisar dattawa guda ɗaya da PDP ke da shi a jihar yana shirin sauya sheƙa zuwa APC, haka ma wasu ‘yan majalisar wakilai uku na shirin bin sahu.

Ya faɗi haka ne sa'ilin da yake jawabi yayin taron shugabanni, dattawa, da masu ruwa da tsaki na APC a Agbor, Ika South, da Ute-Okpu a ƙaramar hukumar Ika North East a ranar Litinin.

APC ba ta bukatar gwamnan Delta da Okowa

Omo Agege ya jaddada cewa APC na maraba da Sanata Ned Nwoko, ‘yan majalisar wakilai, da sauran shugabannin PDP, amma ba ta buƙatar Oborevwori da Okowa su shiga cikinta.

Ya ce:

“Bayan zaɓen 2023, PDP ta yaɗa jita-jita cewa APC ta zama tarihi a Delta. Amma a wannan jihar ce APC ta lashe kujeru biyu na sanata da biyu na Majalisar Wakilai.

Kara karanta wannan

Ana hasashen hadaka, jam'iyyar Kwankwaso ta yi rashi, shugaban NNPP ya koma APC

"A halin yanzu, sanata ɗaya rak ya ragewa PDP wanda shi ma yana shirin dawowa APC. Shin hakan ba yana nuna cewa APC ce jam’iyya mafi ƙarfi ba?"
"A yankin Delta ta Tsakiya ni da Gwamna Oborevwori muka fito amma APC ce ta lashe kujerar Sanata. Daga cikin kujeru uku na Majalisar Wakilai, APC ta samu biyu, sai LP ta samu guda, PDP kuwa ba ta lashe ko ɗaya ba.

APC ta ƙara ƙarfi a jihar Delta

Sanata Omo-Agege ya ƙara da cewa a Majalisar Dokokin Jihar Delta kuwa, daga cikin kujeru tara, APC ta samu biyar, PDP kuwa hudu.

'Dan siyasar ya kuma kwantar wa magoya bayan APC da ke Delta hankali, yana mai cewa za a magance duk wata matsala a cikin jam’iyyar kafin zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa rikicin da PDP ke fama da shi a matakin ƙasa na iya haddasa raguwar tasirin jam’iyyar kafin zaɓen mai zuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun kinkimo hanyar tayar da sabuwar rigima a jam'iyyar PDP ta ƙasa

Omo-Agege ya bayyana cewa nasarorin da manufofin Tinubu suka samu sun sa APC ta zama jam’iyya mafi jan hankali a jihar Delta, wanda ke janyo hankalin manyan ‘yan siyasa zuwa cikinta.

Dalilin da ya sa Sanata Nwoko ya koma APC

Kun ji cewa hadimin gwamnan Delta, Fred Oghenesivbe ya yi zargin cewa Ned Nwoko ya bar PDP ne saboda ya hango ba zai samu tikitin takara ba a zaɓen 2027.

Mista Oghenesivbe ya ce babu wani rikici da ya kori Sanata Nwoko daga jam'iyyar PDP face ganin cewa ba zai samu yadda yake so ba a zaɓe na gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262