Ana Batun Rugujewarta, Gwamnan PDP Ya Fadi Amfanin Rikicin Jam'iyyar

Ana Batun Rugujewarta, Gwamnan PDP Ya Fadi Amfanin Rikicin Jam'iyyar

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan warware rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP
  • Dauda Lawal ya bayyana cewa rikicin da ya dabaibaye PDP zai sanya ta ƙara ƙarfi bayan an magance shi
  • Gwamna Dauda Lawal ya nuna cewa dole ne jam'iyyar PDP ta koyi darasi daga ɗumbin kura-kuran da ta tafka a baya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan rikicin da dabaibaye jam'iyyar PDP.

Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa jam’iyyar za ta ƙara ƙarfi bayan ta shawo kan rikicin da ya addabe ta.

Dauda Lawal ya yi magana kan rikicin PDP
Dauda Lawal ya ce PDP za ta kara karfi bayan rikicinta Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Dauda Lawal ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo kan rasuwar yayansa, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba jam'iyyar PDP?

Kara karanta wannan

Hajjin 2025: Gwamna Radda ya gano hanyar saukakawa maniyyata kashe kudi

Gwamnan ya jaddada cewa dole ne PDP ta koyi darasi daga kurakuran da ta tafka a baya.

Ya bayyana cewa taron gwamnonin jam’iyyar da aka yi a jihar Delta kwanan nan, ya nuna cikakken jajircewarsu wajen dawo da martabar jam’iyyar domin ta jagoranci Najeriya yadda ya kamata.

Gwamna Dauda Lawal ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa PDP za ta shawo kan matsalolin da suka yi mata katutu.

"A siyasa, kodayaushe ana samun matsaloli. Abin da ya faru a Delta kwana biyu da suka gabata ya nuna cewa muna samun ci gaba kuma muna kan turbar daidaita alaƙa da al’umma domin jagorantar ƙasar nan."
“Mu gwamnoni mu ne shugabannin jam’iyyar. Muna da haƙƙi a cikinta, kuma duk abin da muka yanke za a aiwatar da shi. Babu wata matsala da ta addabi PDP.”
“Rikicin da ke gudana ba sabon abu ba ne, ana samun irin sa a sauran jam’iyyu ma. Don haka, wannan abu ne na siyasa kawai.”

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya tuna da iyalan babban jami'in sojan da 'yan Boko Haram suka kashe

"A ƙarshe wannan rikicin zai ƙara mana ƙarfi, domin muna buƙatar mu koyi darasi daga wasu kura-kurai. Hakan na cikin tsarin koyon yadda za a inganta jagoranci."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya faɗi dalilin ziyararsa

Gwamna Dauda Lawal wanda ya je birnin Ibadan tare da mambobin majalisar zartaswarsa, ya jaddada muhimmancin ziyarar da ya kai wa Gwamna Makinde.

"Gwamna Makinde abokina ne na kud da kud, kuma dole ne na zo domin na jajanta masa da ɗaukacin iyalansa kan rasuwar babban yayansa. Kuma na zo nan tare da tawagata."
"Mutuwa dole ce ga kowa, kuma mun zo ne domin ƙarfafa masa gwiwa, tare da tabbatar masa cewa muna tare da shi a wannan mawuyacin lokaci."

- Gwamna Dauda Lawal

APC ta shawarci ƴan Najeriya kan PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ba ƴan Najeriya shawara kan abokiyar hamayyarta ta PDP.

APC ta buƙaci ƴan Najeriya da ka da su sake bari PDP ta hau kan madafun ikon ƙasar nan duba da irin ɓarnar da ta tafka a shekaru da ta kwashe tana mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng