"Za a Tsige Shi daga Shugabancin APC?" An Bayyana Dalilin Naɗa Ganduje a Hukumar FAAN

"Za a Tsige Shi daga Shugabancin APC?" An Bayyana Dalilin Naɗa Ganduje a Hukumar FAAN

  • Mai magana da yawun shugaban APC na ƙasa, Oliver Okpala ya ce naɗin Abdullahi Ganduje a hukumar FAAN alama ce ta girmama mutanen Kano
  • Okpala ya bayyana cewa naɗin na ƙara nuna yadda Bola Tinubu ya yaba da irin gudummuwar da mutanen Kano ke bayarwa a gwamnatinsa
  • Hadimin Ganduje ya buƙaci ƴan Najeriya su zuba ido su ga ci gaban da Ganduje zai kawo a filayen jiragen saman ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Naɗa Dr. Abdullahi Ganduje, shugaban APC na ƙasa a matsayin shugaban Majalisar gudanarwa ta hukumar FAAN alama ce ta girmamawa ga Kano.

Mai magana da yawun Ganduje, Cif Oliver Okpala ne ya bayyana haka yayin da yake martani ga kalaman shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Hadimin shugaban APC ya mayar da martani ga Muhuyi Magaji kan naɗin Ganduje a hukumar FAAN Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya ba Ganduje mukami

Kara karanta wannan

Magana ta zo karshe: Shugaban NYSC ya fadi lokacin fara biyan N77,000

Okpala ya ce naɗin Ganduje a wannan sabon muƙami alama ce ta shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yaba da gudummuwar da Kanawa ke bayarwa, Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba Tinubu ya naɗa Ganduje a matsayin shugaban majalisar gudanarwa ta hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa watau FAAN.

Sai dai yayin da ƴan APC ke murna, shugaban hukumar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta Kano (PCAAC), Muhuyi Magaji Rimingado ya caccaki naɗin Ganduje.

Ganduje: Lokacin siyasar gaba ya wuce

Da yake maida martani ga Rimingado, Okpala ya yi gargadin cewa ya kamata a ce siyasar gaba da rashin mutunta juna ta zama tarihi a Najeriya.

"‘Yan siyasa su fahimci cewa zamanin amfani da dabarun gaba da rashin kishin kasa a siyasa ya wuce,” in ji shi.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su rungumi zaman lafiya da mutunta juna a siyasa, maimakon kiyaya da gaba da ba sa kawo ci gaba a kasa.

Ganduje zai taka rawar gani a sabon mukaminsa

Okpala ya bayyana cewa nadin da aka yi wa Ganduje shaida ce ta amincewar da Tinubu ke da ita a kansa domin ci gaban kasa da kuma dorewar kyakkyawan shugabanci.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya fasa kwai, ya fadi shirin Tinubu kan mika mulki

"Ko masu suka irinsu Rimingado sun yarda ko ba su yarda ba, kokarin da Ganduje ya yi wajen ɗaga ƙimar Kano lokacin da yake gwamna zai ci gaba da kare masa mutunci," in ji shi.

Ganduje zai kawo ci gaba a hukumar FAAN

Ya ce ba shi da kokwanto cewa kishin kasa da sadaukarwar Ganduje za su bayyana a sabon aikinsa, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su zura ido don ganin ci gaba a filayen jiragen saman ƙasar nan.

"Za ku ga manyan sauye-sauye a filayen jiragen saman Najeriya, domin babu shakka Ganduje zai yi aiki tare da masu ruwa da tsaki don kawo ci gaba mai ma'ana," in ji Okpala.

Ya kammala da cewa da a ce shugabannin da suka gabata sun bi sahun shugaba Tinubu wajen daraja wadanda suka yi wa kasa aiki tukuru, da Najeriya ta yi nisa a ci gaba.

Wani jigon APC a Kano, Yusuf Babel ya tabbatarwa Legit Hausa cewa babu shakka Ganduje zai ba mutane mamaki a sabon muƙamin da aka masa.

Ya kuma musanta jita jitar da ake yaɗawa cewa naɗin toshiyar baki ne aka yi wa Ganduje domin raba shi da kujerar shugabancin APC ta kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya tono abin da ƴan Najeriya ba su sani ba game da Bola Tinubu

"Ai babu ko shakka Ganduje ya cancanta da kowane muƙami, yana da ƙwarewa da gogewa, ku duba ci gaban da ya kawo a Kano cikin shekaru takwas.
"Na ji wasu ƴan adawa na cewa wai Tinubu ya masa haka ne saboda yana son cire shi daga shugabancin APC, wannan ba gaskiya ba ne," in ji shi.

APC ta maida martani ga El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta nuna rashin jin daɗinta da kalaman tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Nasiru El-Rufai.

Daraktan yada labaran APC, Bala Ibrahim, ya ce kamata ya yi El-Rufai ya kai korafinsa ga shugabancin jam’iyyar, maimakon fitowa fili yana surutu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262