Bayan ba Hammata Iska a Taron PDP, Sanata Ya Gaji da Lamarinta, Ya Tuba Zuwa APC
- Bayan jita-jita na watanni da dama, Ned Nwoko ya fice daga jam’iyyar PDP kuma ya koma APC, yana mai bayyana rikice-rikicen jam’iyyar a matsayin dalilai
- Sanata Nwoko ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta rabu gida biyu, inda rikicin cikin gida ya hana ci gaba, lamarin da ya sa dole ya sauya sheka
- A cikin wasikar murabus dinsa, Nwoko ya ce yana fatan ci gaba da aiki don amfanin jama’a, duk da cewa ya bar PDP mai adawa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Asaba, Delta - A karshe, Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya fice daga jam’iyyar PDP, ya koma APC.
Nwoko ya bayyana cewa rabuwar kai da rikice-rikice a cikin PDP ne suka sa ya fice daga jam’iyyar, yana mai cewa matsalolin sun gagara warwarewa.

Asali: UGC
Sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC
A cikin wasikar da ya aika wa Shugaban PDP na Mazabar 8, Aniocha ta Arewa, ya tabbatar da murabus dinsa daga jam’iyyar da yake ciki tun 1999, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da barin PDP, Sanata Nwoko ya sha alwashin ci gaba da kawo ababan more rayuwa musamman ga al'ummarsa.
"Na rubuta wannan wasika ne domin sanar da murabus dina daga jam’iyyar PDP, wacce na yi alfahari da ita tun daga lokacin kafuwarta."
"Na yanke wannan shawara ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka hana hadin kai da ci gaba, lamarin da ya hana aiwatar da muradun jama’a."
"A makon nan, a ranar 29 ga Janairun 2025, wasu manyan shugabannin jam’iyyar sun kai ga doke-doke da juna saboda rabuwar kai da rashin jituwa."
- Cewar Sanata Ned Nwoko
Sanata Nwoko ya yi godiya ga PDP
Sanatan Nwoko ya kuma mika godiyarsa ga jam'iyyar kan damar da ta ba shi har ya damu nasara a takarar ɗan Majalisa, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan
'Talauci ne': Ministan Buhari ya fadi dalilin shiga siyasa, ya bugi kirji kan kafa APC
"Na gode wa PDP bisa damar da ta ba ni na tsaya takarar Sanata a 2023, inda na yi aiki da jama’a na don kawo ci gaba."
"Amma yayin kamfen dina, na yi alkawarin inganta rayuwar jama’a, wanda a halin yanzu PDP ba ta ba da damar aiwatar da su."
"Bayan dogon nazari, na yanke shawarar barin jam’iyyar domin in cika alkawuran da na dauka ga mutanena ba tare da shinge ba."
- Sanata Ned Nwoko
Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar PDP
Kun ji cewa jami'an tsaro da suka kunshi sojoji da ƴan sanda sun kai ɗauki babbar hedkwatar PDP ta ƙasa da ke Abuja bayan rigima ta ɓarke a taron BoT.
Rahotanni sun nuna cewa rigimar ta ɓarke ne lokacin da Samuel Anyanwu da Ude-Okeye suka dura wurin taron, lamarin da ya kai ga marin ɗayansu.
Hakan na zuwa ne bayan rikice-rikicen jam'iyyar ya yi kamari, abin da ke neman ɗaiɗaita ta wanda ya jawo taron gaggawa na gwamnonin PDP a jihar Delta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng