Ministan Buhari Ya Tona Asirin Yadda Suka Dauki Hayan Mata domin Kifar da Jonathan

Ministan Buhari Ya Tona Asirin Yadda Suka Dauki Hayan Mata domin Kifar da Jonathan

  • Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana yadda suka biya mata don yin zanga-zanga a lokacin mulkin Goodluck Jonathan
  • Tsohon gwamnan jihar Rivers ya ce ya sha mamaki a lokacin da ya je wurin taron domin gane wa idonsa yadda shirin ke tafiya
  • Amaechi ya caccaki masu jefa kuri'a a Najeriya, yana cewa yawancinsu suna bin 'yan siyasa ne saboda kyauta da alkawarin kudi da suke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya nuna damuwa kan yadda yan siyasa ke yaudarar al'umma a lokacin zabe a kasar.

Amaechi ya tuno yadda suka biya mata farkon yi wa APC rijista domin su yi zanga-zanga a Abuja kan mulkin Goodluck Jonathan.

Amaechi ya tona yadda suka biya mata domin zanga-zanga a mulkin Jonathan
Rotimi Amaechi ya koka kan yadda mata suka yaudare su bayan biyansu domin zanga-zanga a mulkin Jonathan. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Asali: Facebook

Rotimi Amaechi ya soki halayen yan siyasa a Najeriya

Kara karanta wannan

'Talauci ne': Ministan Buhari ya fadi dalilin shiga siyasa, ya bugi kirji kan kafa APC

Amaechi ya bayyana haka ne a Abuja, a wani bidiyo da Punch ta wallafa yayin taron kasa kan karfafa dimokuradiyya, wanda Cibiyar Jagoranci, Dab’i da Ci Gaban Afirka ta shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyo, tsohon gwamnan Rivers ya caccaki halayen masu jefa kuri’a a Najeriya, yana zarginsu da saurin mantuwa da saukin yin biyayya ga ‘yan siyasa saboda kudi.

Mr. Amaechi ya tabbatar da cewa lokacin da aka kafa jam’iyyar APC, manyan jam’iyyar sun biya mata su yi zanga-zanga kan PDP da Gwamnatin Jonathan.

Amaechi ya tono shirin ruguza gwamnatin Jonathan

“Lokacin da aka yi rijistar APC, na ji tsoro kada a murde zabe, mun biya mutane don su kawo mata da sauran jama’a."
"Da na iso da wuri don duba halin da ake ciki, sai na sha mamaki ganin cewa matan da muka kawo suna sanye da rigunan Jonathan a matsayin dan takararsu na shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

- Rotimi Amaechi

Bidiyon maganar da Amaechi ya yi a Abuja

Amaechi ya soki halayen yan siyasa a Najeriya

Kun ji cewa tsohon ministan sufuri a gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan halin ƴan siyasa da ke kan mulki.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ba zai ba da mulki ba, har sai ƴan Najeriya sun nuna da gaske suke yi.

Tsohon gwamnan na Rivers ya buƙaci ƴan Najeriya da su fito a zaɓuka na gaba su kare ƙuri'unsu idan suna son samun shugabanci mai kyau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.