Sanata Shehu Sani Ya Jero 'Miyagun Halayen' Tsohon Gwamnan Kaduna

Sanata Shehu Sani Ya Jero 'Miyagun Halayen' Tsohon Gwamnan Kaduna

  • Tsohon Sanatan yankin Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya dira a kan tsohon gwamnan jiharsa da manyan zarge-zarge
  • Duk da bai kama suna ba, ana zargin Sanatan ya na magana ne a kan Nasir El Rufa'i, wanda ke yi wa APC wankin babban bargo
  • A zarge-zargen da ya yi, Sanata Sani ya zargi tsohon gwamnan da wawashe baitul malin Kaduna, da raba kan jama'a da addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kaduna - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi wa tsohon gwamnan jiharsa shagube.

Duk da bai fito ya kama sunan tsohon gwamnan ba, ana zaton ya yi kalaman ne a kan Nasir El Rufa'i, wanda kalamansa a kan gwamnatin APC ke yamutsa hazo.

Nasir El Rufa'i/Shehu Sani
Shehu Sani ya soki tsohon gwamnan Kaduna Hoto: Nasir El Rufa'i/Shehu Sani
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sanata Shehu Sani ya lissafo wasu halayen tsohon gwamnan Kaduna ba tare da kama suna baro-baro ba.

Kara karanta wannan

'Ka rike matsayinka': El-Rufai ya yi martani ga hadimin Tinubu, ya ce bai son kujerar minista

Shehu Sani ya caccaki tsohon gwamna

Tsohon Sanata, Shehu Sani ya zargi tsohon gwamna a Kaduna da sukar gwamnatin tarayya saboda rashin abin yi da kuncin ba shi da mukami a gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jero wasu daga cikin halayen gwamnan kamar haka:

1. Sani ga Tsohon gwamna: Ka yi mulkin kama karya

Shehu Sani ya yi babban zargi a kan tsohon gwamnan Kaduna da ake zaton Nasir El Rufa'i ne a bangaren tsaro da rashawa.

Ya ce tsohon gwamnan ya rarraba kawunan mutanen jihar da sunan addini, kuma ya samu damar wawashe dukiyar jama'a da tara wa jiharsa bashi.

Sanata Sani ya ce:

"Mutumin da ya wawure dukiyar Kaduna, ya lafta wa al’ummar mu bashin da ba za su iya biya ba, ya raba kan jama'a da addini, ya raba filaye ga abokai da ‘yan uwa, ya ƙi bin umarnin kotu, ya zalunci ‘yan jarida, ya kama mutane saboda suka a kafafen sada zumunta, ya juya garkuwa da mutane zuwa kasuwanci, yanzu yana koyar da wasu yadda za su mulki ƙasa.

Kara karanta wannan

Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

2. An zargi tsohon gwamna da zalunci

Sanata Shehu Sani ya zargi tsohon gwamna a Kaduna da gasa wa jama'a aya a hannu a lokacin da ludayinsa ke kan dawo.

Ya ce:

Lokacin da yake kan mulki a Kaduna, ya yi danniya da zalunci. Yanzu da ya rasa mulki, sai ya rika wa’azin dimokuradiyya ga ƙasar da ya taimaka wajen lalata ta, wawure tattalin arzikinta da zalunta.

3. "Mai fuska biyu," Sanata Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ya zargi tsohon gwamna da bin ta kan 'yan adawa a lokacin da ya ke kan shugabanci.

Ya kara da cewa amma yanzu da ba shi da komai, sai ya koma ya na nuna wa 'yan adawa kauna da bukatar a hade wuri guda.

Shehu Sani ya ce a lokacin da tsohon gwamnan ke ɗasawa wa Tinubu, babu wanda ya fi shi, amma saboda yanzu ba a yi da shi, sai ya koma zagin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

4. "Ba ka da bakin magana," Sanata Sani

Sanata Shehu Sani ya ce tsohon gwamnan da ke caccakar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a yanzu, bai dauki sukar 'yan adawa a lokacin mulkinsa ba.

A kalamansa:

"Mutumin da ke da rashin juriyar sukar ‘yan adawa, ba shi da bakin da zai rika wa'azin shugabanci na gari.

Shehu Sani ya caccaki El Rufa'i

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci mai zafi kan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

Shehu Sani ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mai rashin haƙuri da jurewa suka, wanda ya yi amfani da mulkinsa wajen danniya, amma yanzu yana kiran a koma kan turbar dimokuradiyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel