'Ka Rike Matsayinka: El Rufai Ya Yi Martani ga Hadimin Tinubu, Ya Ce Bai Son Kujerar Minista
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi martani ga hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala kan kalamansa a makon nan
- El-Rufai ya ce tun shekaru 22 da suka gabata, ya kasance Minista inda ya ce ba shi da sha’awar wani matsayi a gwamnatin Tinubu
- Ya ce idan ya kasance a gwamnati, zai bayyana matsaloli da farko a sirri, sannan ya fito fili idan dai ba a dauki matakin gyara ba
- Tsohon gwamnan ya koka cewa wasu ‘yan siyasa da cewa sun zama ‘yan haya, suna kare duk abin da gwamnatin Tinubu ta yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya mayar da martani ga Daniel Bwala, hadimi na musamman ga Bola Tinubu.
Nasir El-Rufai ya bayyana yadda ya fadawa Tinubu bai da sha'awar rike wani muƙami a gwamnatinsa tun da farko.

Asali: Facebook
Bwala ya dura kan El-Rufai bayan sukar APC
El-Rufai ya yi wannan martani a yau Alhamis 30 ga watan Janairun 2025 a shafinsa na X, inda ya soki wasu yan siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya biyo bayan nasiha da hadimin shugaban kasa Bola Tinubu a harkokin yada labarai, Daniel Bwala ya yi ga El-Rufa'i ya ji tsoron Allah.
Daniel Bwala, ya kalubalanci Nasir El-Rufa’i bisa ga irin kalaman da ya yi kan dimokuradiyya da jam’iyyar APC.
El-Rufai ya yi martani ga Daniel Bwala
Tsohon gwamnan ya shawarci Daniel Bwala ya ci gaba da rike muƙaminsa inda ya nuna masa muhimmancin biyayya ga kasa.
Ya kuma tabbatar masa da cewa biyayya ga Ubangiji ya fi yi wa wani dan Adam wanda ake yi domin samun duniya.
"Ina kwana, @BwalaDaniel. Shekaru 22 da suka gabata, na kasance Minista, kuma na bayyana wa Asiwaju tun farko cewa ba ni da sha’awar wani matsayi a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan
Abincin wasu ya kare: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 5, an maye gurbinsu nan take
"Yadda ku da kuka shigo daga baya kuke tada hankali kan abu da ban taba so ba, yana nuna saukin sauya ra’ayinku.
"Da na kasance a gwamnatin Tinubu, da zan fadi matsalata a sirri da farko, sannan in fito fili idan ba a dauki matakin gyara ba, Ni ne daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar, kuma ina da hujjojin da zan bayyana.
"Ka rike matsayinka na mai bada shawara, amma ka tuna cewa biyayya ga Allah da kasa sun fi kowane mutum ko matsayi daraja a rayuwa."
- Nasir El-Rufai
Jigon APC ya kare Nasir El-Rufai
Kun ji cewa Jigon APC, Joe Igbokwe ya bukaci APC ta daidaita da Nasir El-Rufai, yana cewa babu Minista a gwamnati da ya fi shi basira ko jarumta.
Igbokwe ya gargaɗi APC kada ta bar El-Rufai ya koma jam’iyyar adawa, yana jaddada irin gudunmawar da ya bayar a lokacin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan
'Babu Ministan Tinubu da ya fi shi': Jigon APC ya kare El Rufai, ya hango kuskuren jam'iyya
Hakan ya biyo bayan martanin APC ga El-Rufai, inda kakakinta Felix Morka ya zarge shi da rashin kwarewa bayan da ya soki jam’iyyar mai mulki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng