Tsohon Gwamna Ya Tono Abin da Yan Najeriya ba Su Sani ba game da Bola Tinubu

Tsohon Gwamna Ya Tono Abin da Yan Najeriya ba Su Sani ba game da Bola Tinubu

  • Tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande ya ba da labarin yadda ya shawo kan Bola Tinubu har ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023
  • Akande ya bayyana cewa a farko Tinubu bai so neman takara ba saboda matsalolin rashin isassun kudi da larurar ciwon ƙafarsa
  • Dattijon ya ce shi ya tashi ya nufi Legas kuma ya yi nasarar shawo kan Tinubu har ya amince zai nemi zama shugaban ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, ya bayyana rawar da ya taka wajen shawo kan Bola Ahmed Tinubu ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a 2023.

Akande ya ce a farko tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu bai so neman kujerar shugaban ƙasa ba saboda dalilan rashin kudi da shakku a kan kansa.

Kara karanta wannan

'Ka rike matsayinka': El-Rufai ya yi martani ga hadimin Tinubu, ya ce bai son kujerar minista

Bisi Akande.
Bisi Akande ya bayyana yadda ya shawo kan Tinubu ya tsaya takarar shugaban kasa Hoto: Bisi Akande
Asali: Twitter

Bisi Akande ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kan sha'anin kasa da aka wallafa a shafin YouTube na Edmund Obilo a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan ya ce:

"Lokacin da muka haɗu da Tinubu, ya ce mun, Baba kana da isassun kudi? Idan da ina da kuɗin da ake bukata na neman takarar shugaban ƙasa, da na yi gogayya da Ɗangote."

Bola Tinubu ba shi da kuɗin takara

A cewarsa, wannan kalaman da Tinubu ya faɗa masa ya nuna karara cewa ba shi da isassun kuɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Akande ya ƙara da cewa a lokacin Tinubu ba ya ƙaunar tsaya takarar shugaban ƙasa wanda ta kai ga duk wanda ya masa maganar ba su wanyewa lafiya.

"Wasu mutane ne suka kira ni suka ce, na taimaka saboda duk wanda ya yi magana da shi kan shugabancin kasa, sai ya kama faɗa da shi. Don haka na je Legas na same shi," in ji Akande.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

Yadda Akande ya shawo kan Bola Tinubu

Bisi Akande ya ce ya roki Bola Ahmed Tinubu ne ta hanyar yin amfani da al’adar Yarbawa.

"Na ce masa, ba don kai muke so ka zama shugaban kasa ba, kai ba ka da muhimmanci amma a al’adar Yarbawa, idan za a yi bauta, ana amfani da mafi girman dabba ko mafi girman doya.
"Yarbawa suna son su zama shugaban kasa, kuma kai ne ke da dama a yanzu. Za mu yi amfani da kai ne a matsayin hadaya don mu samu shugaban kasa, ba don wani buri naka ba."

Ciwon kafar Tinubu ya so kawo masa cikas

Akande ya ce wannan magana ta razana Bola Tinubu, har ya yi shiru na wani lokaci yana kallonsa.

"Ya dube ni kamar dai ina fama da wata cuta. Sai ya tambaye ni, ‘Baba, yanzu kana cewa in tsaya takara, ya zan yi da ciwon kafata?’"

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

in ji Akande, yana nuni da rashin lafiyar Tinubu.

Akande ya ba shi kwarin gwiwa da cewa,

"Ka tafi ka nemi takara, cikin watanni shida, za ka warke."

Peter Obi ya tsame hannu a haɗakar kwace mulki

Kun ji cewa Peter Obi ya ce ba zai shiga duk wata haɗakar ƴan adawa da aka shirya da nufin ƙwace mulki daga hannun Mai girma Bola Tinubu a 2027.

Obi ya ce abin da ya kamata ƴan siyasa su ba muhimmanci shi ne kawar da talauci, gyara makarantu da asibitoci, da sauran matsaloli da suka addabi Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel