NNPP Ta Roki Tsohon Gwamna Ya Dawo gare Ta bayan Barin APC, Ta Yi Misali da Abba Kabir

NNPP Ta Roki Tsohon Gwamna Ya Dawo gare Ta bayan Barin APC, Ta Yi Misali da Abba Kabir

  • NNPP a jihar Osun ta bayyana shirinta na karɓar tsohon gwamna Rauf Aregbesola da magoya bayansa, yayin da zaɓen gwamna na 2026 ke gabatowa
  • Aregbesola da ƙungiyar Omoluabi Progressives sun fice daga APC saboda wariya, dakatarwa da ƙorafi ba tare da adalci ba, da cin mutuncin tsarinsu
  • Shugaban NNPP a Osun, Tosin Odeyemi, ya bukaci Aregbesola ya shiga jam’iyyar, yana mai cewa hakan zai taimaka mata a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Osogbo, Osun - Jam’iyyar NNPP reshen jihar Osun ta bayyana shirinta na karɓar tsohon gwamna Rauf Aregbesola da magoya bayansa.

Jam'iyyar ta fadi hakan ne yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamna na shekarar 2026 a jihar.

NNPP ta gayyaci tsohon gwamna zuwa gare ta bayan barin APC
Jam'iyyar NNPP ta bude kofa ga tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola da dawo cikinta. Hoto: Rauf Aregbesola.
Asali: Facebook

Aregbesola da magoya bayansa sun bar APC

Shugaban NNPP na jihar Osun, Tosin Odeyemi, ya ce jam’iyyarsu ta cika dukkan ƙa’idojin da Aregbesola da mutanensa ke nema, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Babu Ministan Tinubu da ya fi shi': Jigon APC ya kare El Rufai, ya hango kuskuren jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Lahadi, Aregbesola da magoya bayansa daga ƙungiyar Omoluabi Progressives sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da Sakataren shirye-shiryen ƙungiyar, Oluwaseun Abosede, ya sanya wa hannu, sun ambaci dalilan ficewarsu daga APC.

Daga cikin dalilan akwai wariya, dakatarwa da kora ba tare da adalci ba, da kuma cin mutuncin tsarinsu.

Ƙungiyar Omoluabi Progressives ta bayyana shirinta na shiga wata jam’iyyar siyasa mai irin tunaninsu, domin cigaban jihar Osun da zama misali a Najeriya.

NNPP ta shirya karbar tsohon gwamna daga APC

Shugaban NNPP, Odeyemi daga bisani ya roƙonsu da su haɗa kai da NNPP domin kawo mata nasara a zaben 2026.

Odeyemi ya ce NNPP tana iya kokari wurin gyara kura-kuran tsarin mulki a Najeriya, yana misalta Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano a matsayin misali mai kyau.

Ya ƙara da cewa tarihin Osun ba zai cika ba tare da Aregbesola ba, kuma hakan ne ya sa jam'iyyar APC ke ɗora masa laifin faduwar zaɓensu na 2022.

Kara karanta wannan

Manyan ƙusoshi 2 sun yi arangama a wurin taron majalisar amintattun PDP a Abuja

'Muradunmu iri daya ne' - NNPP ga Aregbesola

Shugaban NNPP ya bayyana cewa Aregbesola dukiya ne a siyasa inda ya ce APC ta san gaskiya, sai dai kawai ba ta son faɗa.

Odeyemi ya bukaci Aregbesola da ya shiga jam’iyyar NNPP domin dawo da martabar Osun, yana mai cewa hakan zai taimaka musu a zaɓen 2026.

Ya ce NNPP da Aregbesola suna da buri ɗaya, wanda shi ne inganta rayuwar al’umma.

Ya buƙaci Aregbesola da magoya bayansa da su shiga NNPP don cigaban jihar Osun, cewar rahoton The Guardian.

APC ta soki tsohon gwamna bayan barin jam'iyya

Kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Osun ta nuna cewa ko a jikinta ba ta damu da ficewar da ƙungiyar Omoluabi ta yi baya daga cikinta.

Ƙungiyar Omoluabi dai wacce ke ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ta tattara ƴan komatsanta ta fice daga APC.

APC ta bayyana cewa ficewarsu ta buɗe hanyar kawo ƙarshen tarihinsu a siyasance kuma ko kaɗan ba ta damu da matakin da suka ɗauka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel