Dogara Ya Tona Asirin 2019: "Yadda Wike Ya Taimaki Bala Ya Zama Gwamnan Bauchi a PDP"
- Yakubu Dogara ya zargi Bala Mohammed da cin amanar Nyesom Wike wanda ya taimake sa da kudin da ya yi yakin neman zabe a 2018
- Tsohon shugaban majalisar wakilan ya yi ikirarin cewa Sanata Bala ya durkusa a gaban Wike a lokacin da ya ba shi tallafin kudin zaben
- Dogara ya ba da labari dalla dalla yadda ministan Abuja na yanzu watau Wike, ya ceci siyasar gwamnan Bauchi, amma ya ci amanarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya ce gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya durƙusa gaban Nyesom Wike yana neman tallafin kuɗi a 2018.
Dogara ya kira gwamnan Bauchi da maci amana, wanda ke “cizon hannun da ya ba shi abinci” bayan samun nasara da taimakon Wike a zaɓen 2019.

Asali: Facebook
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dogara ya yi ikirarin cewa Wike ya dauki nauyin yakin neman zaben Sanata Bala ba tare da neman wani abu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashiya: Yadda rikici ya mamaye Wike da Bala
Wannan tone tonen da tsohon shugaban majalisar ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin shugabanci a jam'iyyar PDP.
Gwamnan Bauchi da Wike sun samu sabani bayan Bala ya zargi ministan da mara wa APC baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Gwamna Bala ya nemi Wike ya sauka daga mukamin ministan Abuja, amma Wike ya maida martani mai zafi.
Wike ya ce shi ma gwamnan Bauchi mayaudari ne, inda ya tunatar da shi yadda ya canza jam’iyya daga ANPP zuwa PDP don amfana da mulkin PDP.
Wike Vs Bala: Dogara ya tuna abin da ya faru a 2018
Dogara ya ce kafin zaɓen fitar da gwanin PDP a 2018, Sanata Bala bai da cikakken goyon baya saboda Abdul Ningi ya na da uwa a gindin murhu a shugabannin jam’iyyar a Bauchi.
Tsohon kakakin majalisar ya ce ya nemi taimakon Wike, wanda ya ba da goyon baya sosai ta hanyar naɗa amintaccensa, Cif Dan Osi Orbih, a matsayin shugaban zaɓen fitar da gwanin.
"Wike ne ya ba da jirgin da aka dauko Cif Dan zuwa Bauchi lokacin zaben fitar da gwanin. Shi ne ya kashe duka kudin, kuma bai nemi a ba shi wani abu ba.
"Bayan Bala Mohammed ya samu tikitin takarar gwamna, sai muka gano ya yi mana karyar cewa yana da kudin da zai gudanar da yakin neman zabensa da na sauran 'yan takara."
- Yakubu Dogara.
An gaza tarawa Bala kudin yakin neman zabe
Yakubu Dogara ya ce Sanata Bala ya yi masu karyar yana da kudi, amma bayan gano gaskiya, suka hadu a gidansa na Wuse 2, Abuja don hada taron tarawa sanatan kudin yakin zabe.
Tsohon shugaban majalisar ya ce sun yi tunanin cewa tunda Bala ya yi minista har na shekaru shida, zai iya samun mutanen da za su tara masa kudi.
Dogara ya ce:
"Mun kafa kwamiti, inda muka kashe N20m wajen hada taron nema masa kudin yakin neman zaben a dakin taro na Lady Kwali da ke otel din Sheraton, Abuja.
"Abin da muka iya tarawa shi ne N48m, kuma idan ka cire N20m da muka kashe na hada taron, za ka ga N28m kadai muka samu."
Dogara, Bala sun sake komawa wajen Wike
Saboda buƙatar ƙarin kuɗi, Dogara da tawagarsa ciki har da Sanata Bala suka ziyarci Nyesom Wike a gidan gwamnatin Fatakwal domin neman taimako.
A lokacin ziyarar, Wike ya koka kan yadda Sanata Bala ya muzguna masa a lokacin suna ministoci a ƙarƙashin mulkin Goodluck Jonathan.
Duk da haka, Dogara ya ce Wike ya yi hakuri kuma ya bayar da tallafin makudan kuɗi don taimakawa yaƙin neman zaɓen Sanata Bala Mohammed.
Dogara ya ce:
"Wike na ganimu tare da Bala Mohammed ya canja fuska. Ya kebe ni a gefe, ya sanar da ni wulakancin da Bala ya yi masa kan raba filaye a Abuja.
"Wike ya ce mun 'na so a ce ka fada mani Bala ne kake wa wannan kokarin, domin ina mai tabbatar maka sai ya ba ku kunya idan ya zama gwamna'."
Bala Mohammed ya durkusa a gaban Wike
Yakubu Dogara ya ce:
"Wike ya kalubalanci Bala kan abin da ya faru tsakaninsu. Bala ya amsa laifinsa amma ya roki gafara da cewar yanzu ya zama nutsattsen mutum. Sanatoci biyu da ke tare da mu a ranar za su zama shaidar haka.
"In gajarce maku labari, a nan gidan gwamnati muka kwana, washe gari Wike ya kira hadiminsa, ya kawo buhun kudi, ya mikawa Bala.
"Da aka mikawa Bala wannan kudi, jikinsa na rawa ya zube har kasa kamar zai sumbaci kasa don murna. Wike ya ba mu kudin da muka gudanar da yakin neman zabe."

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su
Dogara ya ce Wike ne ya bayar da jirgin da aka kwashe su daga Fatakwal zuwa Abuja kuma ba wannan ne lokacin da Wike ya saba taimakonsu ta fuskar sufuri ba.
"Bala ya ci amanar ubangidansa" - Yakubu Dogara
Dogara ya ce abin mamaki ne yadda Bala Mohammed, wanda bai da kuɗin yaƙin neman zaɓe, yanzu ke kiran Wike da suna “mai neman kudi a siyasa.”
Tsohon kakakin ya kwatanta Mohammed da “mai cutar hauka” da kuma “kwararren mai cin amana,” yana zarginsa da cin dunduniya waɗanda suka taimake shi.
"Wadanda suke tunanin ina zafafawa kan lamuran Bala, har suna tausasa ta to yanzu sun fara gane gaskiya, sun dawo daga rakiyar maci amanan.
"Lokaci ba zai ba ni damar lissafa waɗannan Bala ya ci amanarsu ba, ciki har da ubangidansa kuma ubanmu, Baba Waziri, Alhaji Bello Kirki, dattijo kuma tsohon minista a lokacin mulkin Shehu Shagari."
- Yakubu Dogara.
Dogara ya kare Tinubu daga sukar gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya yi martani mai zafi ga gwamnan Bauchi, Bala Mohammed kan sukar shugaba Bola Tinubu.
Dogara ya ce gwamnan ba shi da hurumin sukar shugaban ƙasa kan tattalin arziki ganin yadda ya gaza taɓuka abin kirki a matsayinsa na gwamnan Bauchi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng