'Haba Malam': Hadimin Tinubu Ya Zargi El Rufa'i da Neman Rusa Gwamnati kan Sukar APC

'Haba Malam': Hadimin Tinubu Ya Zargi El Rufa'i da Neman Rusa Gwamnati kan Sukar APC

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya yi gargadi kan barazanar da dimokuradiyya ke fuskanta a Najeriya
  • Biyo bayan kalaman tsohon gwamnan, hadimin shugaba Tinubu, Daniel Bwala, ya mayar da martani ga kalaman El-Rufa’i
  • Nasir El-Rufa’i ya zargi APC da rasa alkibla tare da bayyana matsalolin shugabanci da kaucewa tsarin asali da aka gina ta a kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana damuwarsa kan barazanar da dimokuradiyya ke fuskanta a Najeriya.

A karkashin haka El-Rufa'i ya ce dole ne a dauki matakan gyara domin kare tsarin dimokuradiyya daga rugujewa.

Bwala|El-Rufa'i
Hadimin Tinubu ya bukaci El-Rufa'i ya mayar da takobinsa kan APC. Hoto: Daniel Bwala| Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Biyo bayan lamarin, hadimin shugaban kasa Bola Tinubu a harkokin yada labarai, Daniel Bwala ya yi martani a X tare da nasiha ga El-Rufa'i ya ji tsoron Allah.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa Daniel Bwala ya kalubalanci El-Rufa’i bisa ga irin ra’ayoyin da ya bayyana, inda ya ce bai kamata ya yaki gwamnatin Bola Tinubu ba.

Kalaman da Nasir El-Rufa'i ya yi kan APC

A wani jawabi da El-Rufa’i ya yi, ya bayyana cewa yadda ake tafiyar da mulki a Najeriya a halin yanzu na haifar da barazana ga dimokuradiyya.

Ya ce akwai bukatar jam’iyyun siyasa, musamman wadanda ke adawa, su hadu domin kare dimokuradiyya daga makarkashiya.

Barazana game da zaben 2027

El-Rufa’i ya bayyana wani bincike da ke nuna cewa kashi 75% na masu kada kuri’a a Najeriya ba su da niyyar fita zabe a shekarar 2027.

A karkashin haka ya ce hakan alama ce mai hadari ga makomar dimokuradiyya a Najeriya da bai kamata a bari lamarin ya cigaba ba.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa ana kulla makirci a cikin jam’iyyun adawa kamar PDP da LP, inda ya ce akwai mutane da ke aiki domin ganin jam’iyyun sun rushe.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Ya kuma yi kira ga jam’iyyun adawa su manta da bambance-bambance su, tare da yin aiki tare kamar yadda aka yi wajen kafa jam'iyyar APC.

Martanin Daniel Bwala ga El-Rufa'i

A martanin da ya mayar, Hadimin Shugaban Kasa, Daniel Bwala, ya kalubalanci Nasir El-Rufa’i bisa ga irin kalaman da ya yi kan dimokuradiyya da jam’iyyar APC.

Daniel Bwala ya ce:

"Haba babban yaya!, idan har kana cikin gwamnatin nan, shin za ka furta irin wadannan maganganun?
"Wannar gwamnatin da kake sukar ita ce ka taimaka wajen kafawa, me yasa yanzu kake kokarin ganin an kifar da ita! A ji tsoron Allah."

Bwala ya yi ishara da cewa ya kamata El-Rufa’i ya yi tunani kan gudunmawar da ya bayar a gwamnatin da yake sukar a yanzu.

Za a sauke Ganduje daga shugabancin APC?

A wani rahoton, kun ji cewa an fara rade radin sauke Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC bayan ba shi sabon mukami.

Kara karanta wannan

Sukar APC: Shehu Sani ya yi wa El-Rufai wankin babban bargo

Duk da ba shi mukamin, daraktan yada labaran APC ya ce babu maganar sauke Ganduje duk da magangun da ke ishara da sauke shi da wasu suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel