Ana Rade Radin Sauke Ganduje daga Shugaban APC bayan Tinubu Ya ba Shi Mukami
- Bola Tinubu ya nada Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN, lamarin da ya jawo rade-radin cire shi daga jagorancin APC
- Yan Arewa ta Tsakiya na ci gaba da matsa lamba kan a dawo masu da shugabancin jam’iyyar APC tun bayan murabus din Sanata Abdullahi Adamu
- Biyo bayan rade radin, jam’iyyar APC fitar da matsaya kan tasirin sabon mukamin da shugaba Bola Tinubu ya ba Abdulahi Ganduje ga shugabancinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sabon mukamin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba wa shugaban APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jawo abin magana.
A ranar Juma'a aka nada Abdllahi Ganduje matsayin shugaban majalisar kula da harkokin hukumar Filayen Jiragen Saman Najeriya (FAAN).
Jaridar Daily Trust ta hada rahoto a kan yadda sabon mukamin ya haifar da jita-jitar yiwuwar cire Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya sanar da ba Ganduje mukami tare da wasu shugabannin kwamitocin gudanarwa 42 na hukumomin gwamnatin Najeriya.
Rade-radin sauke Ganduje daga shugabancin APC
Nadin Ganduje ya haifar da muhawara musamman daga yankin Arewa ta Tsakiya, wadanda ke neman a mayar masu da kujerar shugabancin jam’iyyar ta kasa, bayan Sanata Abdullahi Adamu.
Wani daga cikin jiga-jigan jam’iyyar a yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa;
"Muna fuskantar zaben 2027. Ya kamata shugaban kasa ya yi abin da ya dace ta hanyar dawo da shugabancin ga Arewa ta Tsakiya."
Duk da haka, wasu kwararru na ganin jam’iyyar za ta iya amfani da taron NEC mai zuwa domin daukar matakin karshe.
Matsayar APC kan shugabancin Ganduje
Sai dai jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa sabon mukamin Ganduje ba zai shafi aikin shugabancinsa ba.
Daraktan yada labaran jam’iyyar, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa;
"Sabon mukamin ba wani aiki ne na zartarwa ba; ba zai hana Ganduje yin ayyukansa na shugabancin jam’iyya ba."
Bala Ibrahim ya kara da cewa jita-jitar tana daga cikin kokarin rage tasirin Ganduje a jam’iyyar;
"A ko da yaushe suna kirkirar jita-jitar da ba ta tabbata ba."
Bala Ibrahim ya kuma ce koken da Arewa ta Tsakiya ke yi kan tsarin raba mukamai bai dace ba, tun da yanzu yankin na da mukamin babban mashawarci kan harkokin shari’a na jam’iyyar.
A cewar Bala Ibrahim, ya kamata ba Farfesa Kana mukamin ya kasance abin rarrashi ga mutanen Arewa ta Tsakiya.
Hasashen masana siyasa a Najeriya
Masana siyasa irinsu Chief Jackson Lekan Ojo sun bayyana cewa nadin Ganduje wata hanya ce ta rage masa radadin shirin sauke shi daga shugabancin jam'iyyar.
Ya ce shugabancin Ganduje ya sabawa tsarin raba mukami da aka yi kafin zaben 2023, inda Arewa maso Yamma ke da shugabancin majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa.
El-Rufa'i ya caccaki jam'iyyar APC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya caccaki salon tafiyar APC duk da har yanzu yana cikinta.
Nasir El-Rufa'i ya ce a halin yanzu APC ta sauka daga manufar da aka kafa ta tun a karon farko wanda hakan ya kamata ya sanya 'yan adawa haduwa domin ceto Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng