"Ana Saye Ra'ayin 'Yan Adawa da N50m": Atiku Ya Tona Asirin Gwamnatin Tinubu

"Ana Saye Ra'ayin 'Yan Adawa da N50m": Atiku Ya Tona Asirin Gwamnatin Tinubu

  • Atiku Abubakar ya yi gargadin cewa Najeriya na iya rasa dimokiradiyyar da take tutiya da ita idan aka ci gaba da tafiya a haka
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa ya zargi gwamnatin APC da amfani da kudi wajen jan ra'ayin shugabannin jam'iyyun adawa
  • Atiku ya bayyana cewa ya yi gwagwarmaya tsawon shekaru 30, kuma an sha yin yunkurin kashe shi, yana tsallake rijiya da baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi gargadin cewa Najeriya na iya rasa dimokiradiyarta idan ta lamura suka ci gaba da tafiya a haka.

Atiku, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a 2023 karkashin PDP, ya kuma zargi gwamnati mai ci da amfani da kudi wajen saye jagororin jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

Atiku Abubakar ya yi magana kan makomar dimokuradiyyar Najeriya
Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC da saye shugabannin adawa da N50m. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Atiku ya yi wannan jawabin ne ranar Litinin a Abuja, a wani taron ƙarfafa dimokiradiyya, wanda cibiyar LS&D, CDD, WFD, PAACA, da NPC suka shirya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya lissafa matsalolin Najeriya

Atiku Abubakar ya ce:

“Muna cikin wani babban yanayi a wannan karnin na dimokiradiyya. Dole mu yanke shawara ko muna son dimokiradiyya ko mu ba mu sonta."

Ya yi nuni da jam'iyyun siyasa na fuskantar kalubale, inda ya shaida cewa wasu daga cikin waɗannan matsaloli sun koma kan gwamnati.

"Yanzu, gwamnati tana jagorantar jam’iyyun siyasa ne, yayinda ya kamata a ce jam’iyyun siyasar ke jagorantar gwamnati kan abin da ya kamata a yi."

Atiku ya kuma ce majalisar tarayya na da nata matsalolin na kin karbar shawara alhalin ita ce hanyar warware matsalolin kasar ta hanyar tsara doka.

Dan takarar shugaban kasar ya tuno lokacin da ya ba majalisar shawarar yadda za a gyara dokar zabe, amma ya ce ya san ba za ta yi aiki da shawarar ba.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Atiku ya tona asirin gwamnatin APC

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma zargi gwamnatin yanzu da amfani da kudi wajen saye ra'ayin shugabannin jam’iyyun adawa.

"Ina so in faɗi wannan a fili. Na haɗu da shugabannin jam'iyyar adawa a yanzu, suka faɗa mani cewa wannan gwamnati tana ba su N50m kowanne."
“Inda za mu dosa daga nan? Wannan yana nufin cewa idan ba mu yi hankali ba, muna magana da wasu daga cikin ku, amma kuna karɓar N50m daga gwamnatin APC.”

Atiku Abubakar ya tambaya:

"Shin muna son yaƙar dimokiradiyya? Idan ba mu shirya ba, to duk mu tafi gida kawai."

Ya kuma tunatar da kansa game da gwagwarmayarsa ta tsawon shekaru 30, yana fuskantar yunƙurin kisa da kuma zaman ƙaura, amma bai taɓa gajiya ba.

Ya ƙara da cewa ya yi wannan domin ku, yana mai cewa:

"Ba na yin wannan domin kai, na riga na rayu, ina yin wannan ne saboda kun cancanta da kyakkyawar makoma."

Kara karanta wannan

'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya

Atiku ya gano matsaloli a kasafin 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gano wasu manyan matsaloli a kasafin 2025 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

Da yake lissafa matsaloli biyar na kasafin, Atiku Abubakar ya ce gibin N13trn a kasafin kudin 2025 yana nuna rashin tsari mai dorewa da dogaro kan bashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.