"Ba Haka Ya Kamata ba," Peter Obi Ya Kawo Cikas a Shirin Haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

"Ba Haka Ya Kamata ba," Peter Obi Ya Kawo Cikas a Shirin Haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

  • Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan shirye-shiryen haɗa kai da sauran ƴan adawa domin kayar da Bola Tinubu da APC a 2027
  • Ɗan takarar LP a zaɓen 2023 ya cewa ba zai shiga duk wata haɗakar da ke da burin karɓe mulki kaɗai ba, ya ce burinsa a gyara Najeriya
  • Tsohon gwamnan ya kuma yi kira ga mahukunta su gaggauta kawo karshen amfani da kuɗi wajen samun matsayi a siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya musanta shiga haɗin guiwa da nufin kawar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu daga mulki a 2027.

Peter Obi ya ce maganar haɗa maja domin kayar da gwamnatin APC ba ita ce mai muhimmanci a wurinsa ba, burinsa a ceto Najeriya daga ƙalubalen da take ciki.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

Peter Obi da Bola Tinubu.
Peter Obi ya ce batun haɗa maja ba shi ne mafi muhimmanci da ya kamaya ƴan siyasa su maida hankali a kai ba Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Peter Obi ya faɗi hakan ne ranar Litinin a Abuja da yake hira da manema labarai a taron kasa na kwanaki biyu kan karfafa dimokuradiyya, Tribune ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa da kuma APC mai mulki suna tattaunawa kan yiwuwar haɗa maja don kawar da Tinubu daga mulki.

A rahoton Punch, daga cikin waɗanda ake tunanin za su dunƙule wuri guda har da Peter Obi, Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da sauran manyan ƴan siyasa a Najeriya.

Peter Obi ya canza tunani kan haɗa kai

Da yake jawabi, Obi ya ce abin da ya kamata ƴan siyasa su ba muhimmanci shi ne kawar da talauci, gyara makarantu da asibitoci, da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

"A wurina, abinda ya fi muhimmanci shi ne mu tattauna kan Najeriya, ko da za mu haɗa kai, to mu tattauna makomar kasarmu, amma sau da yawa muna watsi da kasar da abin da ya kamata mu yi, mulki kawai muke hange."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

“Ni ba ruwa na da duk wata maja da ake shirin haɗawa da nufin karɓe mulki kaɗai, abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙasar mu Najeriya, taya za mu tsare mutane? Ta ya za mu tallafi talakawa?
“Ta yaya za mu tabbatar da cewa yaranmu suna zuwa makaranta? Wannan shi ne abin da ya fi muhimmanci a yanzu.”

- Peter Obi.

Obi: 'Ya kamata a magance sayen ƙuri'u'

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Obi ya kuma yi kira da a kara kokari wajen hana amfani da kudi a siyasa kamar sayen ƙuri'u.

“Wannan shi ne abin da ya kamata mu cire mu jefar, domin abinda muke yi a yanzu a siyasar Najeriya yana kara buɗe kofar satar kudin al'umma ne kawai.
“Saboda idan na saci kudin talakawa zan iya amfani da su na ci zaɓe na kai ga mulkin da nake kwaɗayi, sannan ina da kariya ba wanda zai tuhume ni, wannan ba komai ba ne face halatta sata," in ji shi.

Kara karanta wannan

Wasu ƴan siyasa na neman canza sunayen talakawan da za a ba tallafin kudi a Najeriya

"Ɓa na kwaɗayin mulki"- Peter Obi

A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya jaddada cewa bai kwallafa rai dole sai ya zama shugaban ƙasa a Najeriya ba.

Obi, wanda ya sha kaye a hannu a APC a zaɓen 2023, ya buƙaci matasa su haɗa kai su yi aiki tukuru wajen samar da shugabanci mai nagarta a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel