'Babban Abu na Shirin Faruwa': Martanin Yan Najeriya da Peter Obi Ya Ziyarci Jigon APC a Kano
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya gana da fitaccen jigon jam’iyyar APC, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura, a Abuja
- Alhaji Zaura ya bayyana cewa ganawar su ta mayar da hankali kan ci gaban jihar Kano da Najeriya baki daya, ba tare da bambancin siyasa ba
- Masu fashin baki sun ce wannan ziyara wani yunkuri ne na Obi don hada kai da manyan ‘yan siyasa gabanin zaben 2027 mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - An yi hasashen siyasa yayin da dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya gana da jigon APC a Abuja.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya gana da Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura, babban jigon jam’iyyar APC.

Asali: Facebook
Zaura ya gana da Obi kan ci gaban Kano
Wannan na kunshe ne a cikin wani rubutu da Zaura ya yi a shafinsa na Facebook inda ya tabbatar da ganawarsa da Obi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaji Zaura a rubutun nasa, ya bayyana cewa tattaunawarsu ta mayar da hankali ne kan hadin gwiwa wajen inganta ci gaban jihar Kano da Najeriya.
Ya ce Gidauniyar AA Zaura za ta yi aiki tare da Obi wajen aiwatar da ayyukan ci gaba a bangarori da dama.
Peter Obi ya kai ziyarar ne a gidan Zaura da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, a wata ziyara ta musamman.
Musabbabin ganawar jigon APC da Peter Obi
"A kokarina na ci gaba da kawo cigaba a Jihar Kano, na ji dadin karɓar bakuncin Mai Girma Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party.
"Baya ga bambancin siyasa, ni da gidauniyar AA Zaura muna fatan yin haɗin gwiwa da shi kan ayyukan da za su inganta ci gaba da ci gaba a Kano da Najeriya baki ɗaya."
- Abdussalam Abdulkarim Zaura



Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da ziyarar
Ziyarar Obi ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin hakan wani mataki ne don hada kai da manyan shugabanni gabanin zaben 2027.
Masu sharhi sun bayyana cewa ziyara za ga iya zama alheri ga Kano da Najeriya yayin da wasu ke zargin akwai siyasa a ciki.
Mubarak Musa Rogo:
"In sha Allahu.shi ne gwamnan Kano 2027."
Mujaheed Sabitu Kode:
"Wani babban abu na zuwa In sha Allah."
Shamsuddeen R Ibrahim:
Obi yaga jajirtacce ne kawai Alaji, Allah mun gode maka da samun uban gida na gari👏."
Peter Obi ya magantu kan makomar siyasarsa
A baya, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya ce zai koma Onitsha ya zama malamin sakandare domin ya ƙarfafa ɗalibai.
Obi ya bayar da tallafin Naira miliyan 25 ga asibitin misiya da yake jihar Anambra, wanda ya ba su kyautarsa lokacin da yake gwamna.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra, Peter Obi ya yi bayani game da shirin da ya yiwa kansa na yin ritaya daga harkokin siyasa Read more:
Asali: Legit.ng