Kusoshin PDP 11 Sun Yi Fito na Fito da Shugaban Jam'iyyar, Sabon Rikici Ya Barke

Kusoshin PDP 11 Sun Yi Fito na Fito da Shugaban Jam'iyyar, Sabon Rikici Ya Barke

  • Mambobi 11 na kwamitin ayyuka na PDP sun yi fito na fito da Umar Damagum kan nadin lauyan da zai kare jam'iyyar a kotun koli
  • 'Yan kwamitin sun bukaci kotun koli ta yi watsi da Dr. J. Y. Musa SAN da Damagum ya nada, inda suka ce tsarin PDP ya saba da nadin
  • A hannu daya kuma, rikici kan wanda zai zama sakataren PDP na kasa ya kara ruruwa yayin da Samuel Anyanwu ya daukaka kara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rikicin jam'iyyar PDP ya koma sabo yayin da mambobin kwamitin ayyuka (NWC) 11 cikin 17 suka juyawa shugabancin Umar Damagum da Samuel Anyanwu baya.

An rahoto cewa wannan sabon rikicin ya samo asali ne kan wakilcin lauyoyin da za su kare jam’iyyar PDP a shari’ar da ke gaban kotun koli.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

'Yan kwamitin ayyuka na PDP sun ki amince da zabin lauyan jam'iyyar da Damagum ya yi
Rikici ya barke a PDP yayin da 'yan kwamitin NWC suka ki amincewa da wani nadin Damagum. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

A baya, rikici ya karade NWC kan shugabancin Damagum da Anyanwu, wanda ya jawo rashin jituwa tsakanin shugabannin jam’iyyar inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin ya kai ga dakatar da Damagum da mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba, kafin shiga tsakani da gwamnonin PDP suka yi.

Sabon rikici ya kunno kai a PDP

Rikicin ya sake kunno kai ne bayan wasikar Damagum ta ranar 20 ga Disamba, 2024, inda ya nada Dr. J. Y. Musa SAN a matsayin lauyar jam'iyyar a shari'ar.

An ce Dr. J. Y. Musa SAN na da kusanci da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, wanda ya kara tayar da jijiyoyin wuya.

Damagum ya bayyana cewa ya rubuta wasikar ne bisa wakilcin NWC don wakiltar jam’iyyar a shari’ar da ke gaban kotun koli.

Mambobin NWC sun kalubalanci Damagum

Sai dai mambobi 11 na NWC, ciki har da Taofeek Arapaja, sun rubuta takardar korafi ga shugaban kotun daukaka kara kan wannan wasika.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

Sun bayyana cewa Damagum ba shi da hurumin nada lauya, domin tsarin PDP ya ce mai ba da shawarar shari’a na kasa ne kadai ke da wannan iko.

Sun bukaci kotun koli ta yi watsi da nadin Dr. J. Y. Musa SAN da ma duk wani lauya da Damagum ya nada.

Sun ce sashe na 42 na kundin tsarin PDP ne ya ba mai ba da shawarar shari’a na kasa damar zabar lauyoyi masu wakiltar jam’iyyar.

Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, ya tabbatar da cewa wasikar su tana da goyon bayan tsarin kundin PDP.

Dawo da mukamin Anyanwu ya jawo rikici

Takaddamar da ake yi kan kujerar sakataren PDP ta jawo cece-kuce tun bayan da Anyanwu ya bar kujerar don takarar gwamnan Imo.

Bayan Anyanwu ya sha kaye a takarar gwamna, kokarinsa na dawo da kujerar sakataren ya kara rura wutar rikicin PDP.

Tuni dai bangaren Kudu maso Gabas na PDP ya amince Sunday Ude-Okoye ya maye gurbin Anyanwu a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa.

Kuma an ce kotun daukaka kara a Enugu ta tabbatar da hukuncin da ya cire Anyanwu a matsayin sakataren kasa, tare da tabbatar da nadin Ude-Okoye.

Kara karanta wannan

"Ana saye ra'ayin 'yan adawa da N50m": Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu

To sai dai shi ma Anyanwu ya daukaka kara tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin.

Rikice-rikicen na iya kassara tasirin PDP

A halin yanzu dai, abubuwa biyu ne suka rikita PDP: rigima kan nada Dr. Musa SAN a matsayin lauya da Damagum ya yi da kuma kokarin Anyanwu na komawa sataren jam'iyyar

Shugabannin jam’iyyar sun ce dole a mutunta tsarin kundin PDP idan har ana so a wanzar da zaman lafiya da daidaito a jam’iyyar.

Ana ganin cewa rikicin da ya shafi shugabanci da hurumin nadin lauyoyi na iya kara girma da nakasa tasirin PDP idan ba a yi sulhu ba cikin gaggawa ba.

Shugaban PDP zai sauka daga mukaminsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, m,ataimakan shugabannin PDP na ƙasa sun nuna cikakken goyon bayansu ga shugaban jam’iyyar, Umar Damagum.

Timothy Osadolor, mataimakin shugaban matasan PDP, ya tabbatar da cewa Damagum zai ci gaba da rike shugabanci har zuwa Disamba 2025, lokacin da wa’adinsa zai kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com