Faɗa Ya Ɓarke Tsakanin Gwamna da Ministan Tinubu, An Fara Musayar Baƙaƙen Kalamai
- Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, da ministan Abuja, Nyesom Wike, sun zafafa musayar bakaken kalamai kan zargin cin amanar PDP
- Gwamna Bala ya ce Wike ya kasance ɗan siyasa marar alkibla da rashin gaskiya, wanda ke amfani da rikicin PDP wajen cima burinsa
- Wike ya mayar da martani, yana zargin gwamnan Bauchi da cin amanar iyayen gidansa na siyasa musamman tsohon gwamna, Isa Yuguda
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rigimar gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, da ministan Abuja, Nyesom Wike, ta dauki sabon salo da suka fara musayar bakaken kalamai.
Gwamna Bala ya yi ikirarin cewa za a tuna da Wike ne kawai a matsayin matsayin ɗan siyasa mai cin amana da ya yiwa PDP butulci.

Asali: Twitter
Shi kuma Nyesom Wike ya zargi Sanata Bala da rashin iya jagoranci a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin PDP, inji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan
Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed ya bayyana cewa Wike na neman suna amma baya kawo cigaba mai amfani, yana mai zargin shi da zama dan siyasa mai son zuciya fiye da ci gaban jama'a.
Gwamnan Bauchi ya caccaki ministan Abuja
Gwamna Bala, a cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa kan kafofin watsa labarai, Mukhtar Gidado, ya ce Wike mutum ne marar alkibla.
Sanata Bala ya bayyana Wike a matsayin ɗan siyasa mai cike da son zuciya, wanda ke kokarin tarwatsa PDP - jam'iyyar da ta inganta matsayinsa.
Ya ce Wike mutum ne da ya dogara da hada husuma da kawo rarrabuwar kawuna, yana mai bayyana shi a matsayin ɗan siyasa mai saurin canja ra'ayi don bukatar kansa.
A bangaren abokantaka da mulki, gwamnan ya yi wa Wike martani da cewa abokantaka ba ita ce ke gina shugabanci ba, illa cancanta da hangen nesa.
Wike ya mayarwa gwamnan Bauchi martani
Amma Wike ya mayar da martani, ta bakin mai taimaka masa kan kafofin sadarwa, Lere Olayinka, yana mai bayyana Mohammed a matsayin ɗan siyasa mai son kai.

Kara karanta wannan
Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe
Ya tuna wa Mohammed yadda ya bar tsohon ubangidan siyasarsa, Isa Yuguda, da kuma Muhammadu Buhari a shekarun baya saboda son kai.
Olayinka ya ce Sanata Bala yana sukar Wike ne kawai don samun amincewar PDP ta ba shi tikitin shugaban kasa na PDP a 2027, wanda ya ce ba zai cimma hakan ba.
Ya ce Bala Mohammed ya karbi mukamin shugaban kungiyar gwamnonin PDP saboda son kai, duk da cewa ya kamata kudancin kasar ne zai rike matsayin.
Olayinka ya ce Mohammed bai iya kawo hadin kai a PDP ba, yana mai zargin shi da kawo rabuwar kai a kwamitin gudanarwar jam’iyyar (NWC).
Gwamnan Bauchi ya gana da Nyesom Wike
Kafin rigima ta yi tsamari tsakaninsu, Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi ganawar sirri da ministan Abuja, Nyesom Wike.
An rahoto cewa Bala Mohammed ya gana da Wike ne domin dinke barakar da ke tsakanin PDP da gwamnonin G5, wadanda aka zarga da kin goyawa jam'iyyar baya a 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng