Fitattun Ƴan Siyasar Kano 3 da Tinubu Ya Nada Jagororin Manyan Hukumomin Gwamnati

Fitattun Ƴan Siyasar Kano 3 da Tinubu Ya Nada Jagororin Manyan Hukumomin Gwamnati

Kano - Shugaba Bola Tinubu ya nada shugabannin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya 42 da kuma sakataren hukumar CDIPB.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa Tinubu ya kuma nada sabon shugaba (MD) na hukumar NRC da shugaba (DG) na hukumar NBTI.

Wasu manyan 'yan siyasar Kano da Tinubu ya nada muhimman mukamai
Shugaba Bola Tinubu ya sake ba Ganduje da Nasiru Gawuna wasu sababbin mukamai. Hoto: @OfficialAPCNg, @HadizaNasirAhm2
Asali: Twitter

Sababbin nade naden Tinubu daga Kano

Shugaba Tinubu ya umarci shugabannin gudanarwar da kada su tsoma baki cikin tafiyar da ayyukan hukumomin, yana mai bayyana cewa matsayinsu ba na aiki kai tsaye ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar ta nuna cewa dukkanin nade-naden sun fara aiki nan take.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta yi tsokaci kan manyan 'yan siyasa uku daga jihar Kano da Shugaba Tinubu ya nada shugabanni a wasu mahimman hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

An dai san Kano a matsayin daya daga cikin jihohin da ke da matukar muhimmanci a fagen siyasar Najeriya.

1. Janar Jubril Abdulmalik

Shugaba Tinubu ya amince da nadin Janar Jibril Abdulmalik (mai ritaya), wanda dan asalin Kano ne, a matsayin sakataren hukumar CDIPB.

Masani a harkokin tsaro, Janar Abdulmalik ya yi aikin soja da wasu hukumomin tsaro, sannan ya kasance daraktan tsaro a kwamitin yakin neman zaben Tinubu-Shettima na 2023.

Kungiyar Renewed Hope United Kingdom ta yi amma da cewa:

"Janar Abdulmalik ya dace da jagorantar tsara manufofi da dabarun aiki ga hukumomin tsaro da ba na soja ba, domin tabbatar da ingantaccen tsaro, kula da iyakoki, da kuma gyaran gidajen yari."

Kungiyar Renewed Hope United Kingdom ta wallafa a shafinta na X cewa:

"Nadinsa ya nuna aniyar Shugaba Tinubu na karfafa tsarin tsaron cikin gida Najeriya ta hanyar nada kwararru da gogaggu a mahimman mukamai."

Kara karanta wannan

Ana rade radin sauke Ganduje daga shugaban APC bayan Tinubu ya ba shi mukami

2. Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya yi gwamnan jihar Kano daga 2015 zuwa 2023. A baya ya taba zama mataimakin gwamna ga Rabiu Musa Kwankwaso sau biyu, daga 1999 zuwa 2003 da kuma daga 2011 zuwa 2015.

Abdullahi Umar Ganduje kusa ne a siyar Najeriya daga jihar Kano kuma kuma shugaban jam’iyya mai mulki ta APC na kasa.

A watan Agustan 2023, kwamitin zartarwa na kasa (NEC) ya nada Ganduje a matsayin shugaban APC na kasa bayan murabus din Abdullahi Adamu.

Ganduje ya kasance babban abokin siyasa ne ga shugaba Tinubu.

A watan Janairun 2025, Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN, wani reshe a ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya.

3. Nasir Yusuf Gawuna

Gawuna, kwararren ma’aikacin lafiya kuma dan siyasa ne, wanda Shugaba Tinubu ya nada shi shugaban hukumar lamunin gidaje ta Najeriya.

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Wannan hukuma ce da ke bayar da lamuni na dogon zango ga cibiyoyin bayar da lamunin gidaje a Najeriya.

A watan Mayun 2022, Gawuna ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben jihar Kano na 2023, amma ya sha kaye daga dan takarar NNPP.

Nasir Yusuf Gawuna ya rike matsayin mataimakin gwamnan Kano karkashin Ganduje daga 2018 zuwa 2023.

Bayan nadin Gawuna, magoya bayan APC da dama sun nuna farin cikinsu a shafukan sada zumunta.

Bashir Ahmad, tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafafen yada labarai na zamani, ya shiga jerin masu taya murna.

Ya rubuta a shafinsa na X a yammacin Juma’a, 24 ga Janairu cewa:

"Wannan sakon taya murna ne ga Dakta Nasiru Gawuna bisa nadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa a matsayin shugaban hukumar lamunin gidaje ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

"Ina masa fatan nasara a wannan muhimmin aiki, na san zai yi aiki tukuru don ingantawa da samar da gidaje masu araha ga al’ummar Najeriya."

Ganduje zai yi takara da Tinubu a 2027?

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Abdullahi Umar Ganduje ya karyata masu yada jita jitar cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa wanda kuma shi ne tsohon gwamnan Kano ya ce ba shi da wata alaka da fastocin da ake yawo da su na neman takararsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.