An Yada Hotunan Ganawar Yahaya Bello da Wike, an Yi Hasashen Dalilin Haɗuwar Su
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kai ziyara ga Ministan FCT, Nyesom Wike, a gidansa da ke Abuja, a yau Alhamis
- Bello yana fuskantar shari'o'in zamba ta biliyoyin Naira da EFCC ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da kuma kotun Abuja
- Masana siyasa na ganin wannan ziyara wata hanya ce ta neman hadin kai da manyan mambobin gwamnatin Bola Tinubu domin dawo da karfinsa a APC
- Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu sahihan bayanai kan ainihin musabbabin ganawar da suka yi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kai ziyara ga Ministan FCT, Nyesom Wike, a gidansa da ke birnin Abuja.
Yahaya Bello ya ziyarci tsohon gwamnan Rivers a yau Alhamis 23 ga watan Janairun 2025 a birnin Tarayya.

Source: Facebook
Matsalar zargin cin hanci kan Yahaya Bello
Leadership ta ruwaito cewa Bello bai je wannan ziyara shi kadai ba; yana tare da magajinsa kuma gwamna mai ci na jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da tsohon gwamna, Yahaya Bello ke karkashin beli game da shari’o’in zamba ta biliyoyin Naira da EFCC ta shigar a kotu.
Wadannan shari'o'i suna gudana a Babbar Kotun Tarayya da kuma kotun Abuja, bayan kare mulkinsa a 2024.
An yi ta kai ruwa rana da tsohon gwamnan da Hukumar EFCC kan zargin badakalar da ake yi kansa inda daga bisani ya kawo kansa gare ta a birnin Abuja.
Yahaya Bello ya yi kira kan zaman lafiya
Bayan fitowarsa daga kurkuku tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi kira ga zaman lafiya da hadin kai domin ci gaban jihar da kasa baki daya.

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su
Yahaya Bello ya nemi goyon bayan al’ummar jihar Kogi ga gwamna Ahmed Usman Ododo da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Hasashen da ake yi kan ganawar Bello, Wike
Masana sun yi hasashen cewa wannan ziyara wata hanya ce ta neman sababbin abokai a cikin gwamnatin Bola Tinubu.
Ana ganin hakan bai rasa nasaba da neman dawo da martabarsa musamman a APC duba da watsi da ake zargin gwamnatin ta yi da shi da wasu jiga-jiganta.
Bello yana zargin wasu manyan mambobin APC da zama sanadiyyar matsalolinsa, wanda ya yi tasiri wajen kaucewa harkokin jam’iyyar.

Source: Facebook

Source: Facebook

Source: Facebook
Fubara ya caccaki tsohon mai gidansa, Wike
A baya, kun ji cewa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa 'yan majalisar PDP da suka sauya sheka zuwa APC sun rasa kujerunsu dindindin.
Fubara ya ce babu wata majalisa da ta wanzu a jihar sai wanda Victor Oko-Jumbo ke jagoranta tare da sauran ‘yan majalisarsa uku.
Ya jaddada cewa ya sha wulakanci daga mutanen Nyesom Wike amma yanzu burinsa shi ne kare muradun jihar Rivers da tabbatar da gaskiya a mulki.
Asali: Legit.ng
