2027: Tsofaffin Gwamnnonin PDP 5 da Za Su Iya Goyon Bayan Tinubu Idan Ya Nemi Tazarce
- Yayinda Najeriya ke ci gaba da gudanar da dimokuradiyya ba tare da tangarda ba, kasar na tunkarar babban zaben shekarar 2027
- Ana ci gaba da tattaunawa game da zaben 2027, zabe na takwas tun bayan dawowar Najeriya kan turbar dimokuradiyya a 1999
- Legit Hausa ta jero wasu tsofaffin gwamnonin PDP da za su iya goyon bayan shugaba Bola Tinubu idan ya nemi tazarce a mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Akwai yiwuwar cewar shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu zai nemi tazarce idan wa'adinsa ya kare a shekarar 2027.
Tun da ya shiga siyasa, an ce shugaba Bola Ahmed Tinubu bai taba hada kai da jam’iyyar adawa ta PDP ba.

Asali: Twitter
Sai dai kuma babban jigo a jam’iyyar ta APC na iya samun goyon bayan wasu ’yan siyasa da suka jagoranci jihohin Najeriya a karkashin PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng Hausa ta jera wadannan mutanen.
1. George Akume
Rahotanni sun bayyana cewa Akume ya rike matsayin gwamnan jihar Benue na wa'adi biyu, daga 1999 zuwa 2007, a karkashin PDP.
Shi ne ministan ayyukan na musamman da harkokin gwamnati daga 2019 zuwa 2023 a zamanin shugaban Muhammadu Buhari.
Akume ya kasance sanata daga 2007 zuwa 2019 kuma shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai daga 2011 zuwa 2015.
A halin yanzu, Akume shi ne sakataren gwamnatin tarayya (SGF) kuma yana iya goyon bayan sake zaben Tinubu a 2027.
2. Chimaroke Nnamani
Nnamani ya kasance likita kuma dan siyasa, wanda ya zama gwamnan jihar Enugu daga 1999 zuwa 2007 a karkashin jam'iyyar PDP.
Chimaroke Nnamani ya zama sanatan yankin Enugu ta Gabas daga 2007 zuwa 2011 sannan an sake zabenshi a 2019.
The Punch ta ruwaito Nnamani yana cewa ya goyi bayan Tinubu a 2023 saboda rashin adalci ya fuskanta daga PDP.
Akwai yiwuwar cewar tsohon gwamnan na Enugu zai goyi bayan Tinubu a 2027 musamman ganin yadda yake kare shugaban kasar a fili.
3. Samuel Ortom
Ortom ya zama ministan harkokin kasuwanci da zuba jari a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.
Ya zama gwamnan Benue a APC a shekarar 2015, amma daga baya ya koma PDP, sannan aka sake zabe shi a 2019.
Mulkin Ortom ya kare a 2023. A Janairu 2024, Ortom ya ce tawagar G5 za ta goyi bayan Tinubu idan ya nemi sake zabe a 2027.
4. Nyesom Wike
A watan Nuwamban 2023, Wike ya sha alwashin ba zai tsaya takara a zaben shugaban kasa na 2027 ba, domin ba zai kara da Shugaba Tinubu ba.
Da yake magana a wani shirin kai tsaye na gidan talbijin wanda Legit Hausa ta bibiya, Wike ya ce shi dan halas ne don haka ba zai yi takara a 2027 ba.

Kara karanta wannan
'Babban abu na shirin faruwa': Martanin yan Najeriya da Peter Obi ya ziyarci jigon APC a Kano
Kafin wannan lokacin, Wike, jigon jam’iyyar PDP, ya yi alkawarin tarawa Shugaba Tinubu kuri'u a zabe mai zuwa, inda ya ce jam'iyyun da suka samu kuri'u 2,000 a zaben 2023, ba za su samu komai a 2027 ba.
5. Ayodele Fayose
Fayose, wanda ya jagoranci jihar Ekiti a matsayin gwamna na PDP, ya tabbatar da cewa ya taka rawar gani a wajen faduwar jam'iyyar PDP a zaben 2023.
Rahoton Channels TV ya ce Fayose ya yi hamayya da Atiku Abubakar a zaben 25 ga Fabrairu, 2023 inda ya tarawa Tinubu ruwan kuri'u.
Sai dai idan har zai canza shawara a lokacin zaben 2027, ana kyautata zaton tsohon gwamnan jihar na Ekiti zai goyi bayan Tinubu da APC.
"Tinubu zai iya lashe zaben 2027" - Omokri
A wani labarin, mun ruwaito cewa Reno Omokri, tsohon hadimin shugaban kasa, ya yi magana kan yiyuwar Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zabe a 2027.
Omokri ya yabawa Tinubu bisa iya juya tsofaffin abokan gaba zuwa abokai, tare da amfani da wannan dabarar wajen cimma burinsa na siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng