Malamin Addini Ya Ragargaji Tinubu bayan Ganawa da Gwamnan Bauchi
- Shahararren Fasto, Johnson Suleman ya danganta matsalolin tattalin arzikin Najeriya da zaben 2023, yana cewa rashin kyakkyawan zabi ya jawo haka
- Johnson Suleman ya yi kakkausar suka kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu, musamman kan yadda aka tafiyar da bangaren man fetur
- Gwamna Bala Mohammed ya ce manufofin Tinubu sun jefa Najeriya cikin mummunan hali, yana mai jan hankalin kan daukar tsauraran matakai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Babban Faston cocin Omega Fire Ministries, Johnson Suleman ya ce wahalhalun rayuwa da 'yan Najeriya ke ciki sakamakon mummunan zaben shugabanni ne a 2023.
Fasto Johnson Suleman ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka shirya a jihar Bauchi na tsawon kwanaki biyu.
Hadimin gwamnan jihar Bauchi a fannin yada labarai, Lawal Muazu ya wallafa a Facebook cewa Faston ya ziyarci gidan gwamnati tare da gana wa da gwamna Bala Mohammed.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alakar wahalar rayuwa da zaben 2023
Da yake magana da manema labarai a gidan gwamnatin Bauchi, Fasto Suleman ya yi kakkausar suka kan yadda 'yan Najeriya suka zabi shugabanni ba tare da lura da cancanta ba.
"'Yan Najeriya sun cancanci halin wahalar rayuwa da suke fuskanta a halin yanzu. Kafin zabe, mun yi kira, mun yi gargadi, amma mutane sun yi biris,"
- Fasto Johnson Suleman
Ya zargi shugaba Bola Tinubu da rashin gabatar da ingantacciyar manufa kafin zabe, yana mai cewa ya dogara ne kawai da zancen"Emilokan."
Sukar manufofin gwamnatin Bola Tinubu
Fasto Suleman ya bayyana cewa manufofin gwamnatin Tinubu suna kara jefa tattalin arzikin kasar cikin mummunan hali, musamman kan bangaren man fetur.
"An lalata bangaren man fetur. A shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa, ba zan yi mamaki ba idan Najeriya ba ta farfado ba. Abu daya kawai za mu iya yi yanzu shi ne addu'a,"
- Fasto Suleman
Jaridar Punch ta wallafa cewa Faston ya yi kira ga 'yan Najeriya da su dauki darasi daga abin da ke faruwa a yanzu domin guje wa irin wannan kuskuren a zaben shekarar 2027.
Bala Mohammed ya soki gwamnatin Tinubu
A nasa bangaren, Gwamna Bala Mohammed ya yi suka kan manufofin gwamnatin tarayya, yana mai cewa babu hangen nesa a cikin su.
Sanata Bala Mohammed ya ce tsare tsaren shugaba Tinubu ba su da kyakkyawar manufa kuma sun jefa Najeriya kan hanyar lalacewa.
Gwamnan ya bayyana cewa yana goyon bayan tsare tsaren, amma ya ce gyaran da ake bukata ya kasance wanda zai amfani kasa gaba daya, ba wai wanda zai kara dagula al'amura ba.
Bala Mohammed zai cigaba da sukar Tinubu
Gwamna Mohammed ya jaddada cewa zai ci gaba da yin suka kan duk wata manufa da ba za ta amfani al'ummar Najeriya ba.
Sanata Bala Mohamed ya ce 'yan Najeriya sun cancanci samun cigaba, kuma ba zai yi shiru ba idan ya ga kura-kuran gwamnatin tarayya.
Ya bayyana cewa ya kamata a rika fifita bukatun al'umma wajen tsara manufofin gwamnati domin tabbatar da samun ci gaba mai dorewa.
Gwamna ya zargi Tinubu da rusa 'yan adawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce Bola Tinubu na amfani da wata hanya domin samun nasara a 2027.
Gwamna Bala Mohammed ya bukaci shugaban kasar da ya daina amfani da ministocinsa wajen sukar 'yan adawa ba tare da wani dalili ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng