Shugabannin PDP da APC Sun Harbi Juna da Maganganu bayan Hari a Kotun Edo

Shugabannin PDP da APC Sun Harbi Juna da Maganganu bayan Hari a Kotun Edo

  • Jam'iyyun APC da PDP sun yi musayar kalamai kan harbe-harbe da suka tayar da hankula a kusa da kotun da ake shari'ar zaben Edo
  • Rahotanni sun nuna cewa shugabannin jam'iyyun sun zargi juna da yin amfani da 'yan daba domin kawo rikici yayin zaman kotun
  • Kotun Zaben Edo ta fara sauraren karar da ke kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar na 2024 da jam'iyyar APC ta yi nasara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - A ranar Laraba, harbe-harbe sun tayar da hankula kusa da kotun zaben Edo da ke Benin, yayin da ake sauraron karar kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar.

Jam'iyyun APC da PDP sun yi musayar kalamai, suna zargin juna da hannu a harin da aka ce wasu 'yan daba da suka rufe fuskokinsu suka kai.

Kara karanta wannan

Tsofaffin sojoji sun fallasa masu ba Boko Haram makamai da kudi

APC da PDP
APC da PDP sun yi musayar yawu kan shari'ar zaben Edo. Hoto: Official PDP|Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta hada rahoto kan yadda manyan jam'iyyun suka jefi juna da kalamai bayan harin 'yan bindigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi harbe-harbe a jihar Edo

Rahotanni sun nuna cewa wani matashi ya fito daga wata mota kirar Toyota Hilux marar rijista, yana harbi sama a kusa da kotun.

Mutane sun shiga rudani, yayin da matashin ke ihu yana cewa, “Ku dawo mana da abin da muka zaba” kafin ya shiga motar tare da wani mutum, suka fice daga wurin.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa harbe-harben sun tilasta wa masu wucewa guduwa domin tsira, yayin da jami’an ‘yan sanda da ke wurin suka kasa daukar mataki kan lamarin.

Jam'iyyar APC ta zargi PDP kan harin Edo

Shugaban APC na jihar Edo, Jarrett Tenebe ya bayyana cewa 'ya 'yan PDP ne suka kitsa harin domin tayar da hankali a wurin kotun zaben.

Kara karanta wannan

Alkali da lauyoyi sun tsure yayin da aka fara harbe harbe ana tsaka da shari'a a kotu

A cewar shugaban;

“Abin da ya faru a yau a wurin kotun sauraron koke-koken zabe abin takaici ne kuma ba za a lamunce shi ba.
"Kotun zabe wuri ne na adalci, saboda haka duk wani nau’i na tashin hankali a cikinta zai kawo tarnaki ga tsarin shari’a.”

Ya kara da cewa amfani da tashin hankali wajen warware rikici ba abu ne mai karbuwa ba, tare da yin kira ga dukkan bangarorin su guji irin wannan dabi'a.

Harin Edo: PDP ta musanta zargin APC

A nata martanin, shugabar kwamitin rikon kwarya ta PDP a jihar, Tony Aziegbemi, ta musanta zargin da APC ta yi.

“Ba mu da hannu a harbe-sharben da suka faru a kusa da kotun zabe. Wannan wani shiri ne na APC na bata sunan PDP da kuma kawo cikas ga shari’ar da muke yi na kwato hakkinmu."

- Tony Aziegbemi

Jam'iyyar ta kuma bayyana cewa APC na amfani da dabarun siyasa domin hana PDP cin nasara a kotun.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Katsina: Ƴan bindiga sun harbi likita, sun sace mutane

Dalilin kai APC kara kotu a zaben Edo

Mai Shari’a Wilfred Kpochi ya fara sauraron shari’o’i guda bakwai da ke kalubalantar nasarar Gwamna Monday Okpebholo na APC.

Hukumar INEC ta bayyana Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 291,667 yayin da dan takarar PDP, Asue Ighodalo ya samu kuri'u 247,274.

Saboda rashin amincewa da sakamakon zaben, PDP da wasu jam’iyyu guda biyar sun kai karar INEC da Okpebholo gaban kotu.

Yadda shaidu suka bayyana a kotu

A ranar Laraba, Dr Bright Enabulele na jam’iyyar AP ya gabatar da shaidu uku domin kare karar da ya shigar.

Shaidun sun bayyana cewa an yi zaben a wasu mazabu cikin rashin da’a, ciki har da cika akwatunan zabe da kuri’un bogi.

Shaidun sun kuma bayyana rashin bai wa wakilan jam’iyyun katin tantancewa daga INEC a wasu wurare, wanda suka ce ya kara dagula tsarin zaben.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

Gwamnan Edo ya dakatar da ciyamomi

A wani rahoton, kun ji cewa an samu sabani tsakanin gwamnatin jihar Edo da wasu shugabannin Kananan hukumomi.

Legit ta ruwaito cewa gwamnan jihar ya zargi shugabannin kananan hukumomi da raba kudi har Naira biliyan 12 ga 'yan PDP domin rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng