Zabe: ‘Yan sanda sun kama wani mutum da kuri’un bogi a Sokoto

Zabe: ‘Yan sanda sun kama wani mutum da kuri’un bogi a Sokoto

- ‘Yan sanda a jihar Sokoto sun kama wani mutum mai suna Shehu Maidamma bisa zargin sa da mallakar wasu kuri’un zabe na bogi

- Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto, Muhammad Sadiq, ya tabbatar da hakan ga manema labarai

- Kakakin INEC a jihar Sokoto, Muhammad Musa, ya tabbatar da cewar kuri’un da aka samu tare da mutumin ba nag aske ba ne

Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta kama wani mutum mai suna Shehu Maidamma bisa zargin sa da mallakar wasu kuri’un zabe na bogi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto, Muhammad Sadiq, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau, Litinin, a Sokoto.

Mista Sadiq ya ce: “rundunar ‘yan sanda na son wayar da kan jama’a a kan jita-jitar da ke yawo a gari a kan kama wani mutum da kuri’un zabe.

“A ranar Lahadi da ta gabata ne wasu jami’an ‘yan sanda yayin sintiri su ka kama wani mutum mai suna Shehu Maidamma da kuri’un bogi da jam’iyyar PDP su ka buga.

Zabe: ‘Yan sanda sun kama wani mutum da kuri’un bogi a Sokoto
‘Yan sanda sun kama wani mutum da kuri’un bogi a Sokoto
Asali: Facebook

“Kuri’un na gwaji ne, ba na gaske ba ne kamar yadda hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta tabbatar.

“A saboda haka, i na kira ga jama’a da su kwantar da hankalin su domin jami’an tsaro na aiki tare da INEC domin tabbatar da an yi zabe mai tsafta kuma cikin zaman lafiya a fadin kasa baki daya.”

DUBA WANNAN: Zabe: Buba Galadima ya yi wa ubangiji izgili, bidiyo

A bangaren sa, kakakin INEC a jihar Sokoto, Muhammad Musa, ya tabbatar da cewar kuri’un da aka samu tare da mutumin ba nag aske ba ne.

Mista Musa ya ce: “jam’iyyun siyasa na da hakkin wayar da kan jama’a a kan yadda ya kamata su kada kuri’a sannan ya kara da cewa amma tuni an dakatar da yakin nemn zabe tun 12:00 na ranar juma’a, 15 ga watan Fabrairu.

Har yanzu jam’iyyar PDP ba ta mayar da martani a kan faruwar wannan lamari ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel