'Yan Majalisar Arewa Sun Shirya Tirjiya ga Tinubu kan Kudirin Haraji
- ’Yan majalisa daga yankin Arewa sun shirya nuna tirjiya kan kudirin gyaran haraji da ke gaban majalisa yayin da za su dawo hutu
- Hakan na zuwa ne bayan shugaba Bola Tinubu ya nace kan cewa gyaran haraji zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya
- Ana sa ran tsare-tsaren kasafin kuɗin 2025 da kudirin gyaran haraji za su mamaye muhawarar majalisar yayin da ta koma yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da majalisar ƙasa ke shirin komawa zama, zancen kudirin gyaran haraji na cigaba da jan hankali, musamman daga bangaren ’yan majalisar Arewa.
’Yan majalisar Arewa na zargin cewa kudirin yana tattare da matsaloli da suka haɗa da rashin tattaunawa, lokaci mara dacewa, da tsarin da zai cutar da tattalin arzikin yankin.
Jaridar Daily Trust ta wallafa rahoto a kan yadda 'yan majalisar Arewa suka shirya tirjiya ga kudirin a zauren majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji da matsalar da ake fuskanta
Kudirin gyaran haraji ya riga ya wuce karatu na biyu a zauren majalisar dattawa kafin a tafi hutun Kirsimeti, amma an dakatar da ci gaba da muhawara kan kudirin.
Shugaban marasa rinjaye daga mazabar Benue ta Kudu, Sanata Abba Moro, yana jagorantar wani kwamiti domin tattaunawa da Antoni-Janar na Tarayya kan kudirin.
Wannan yunkuri ya zo ne domin magance damuwar da aka bayyana game da kudirin, musamman daga Arewa.
Sanata Ali Ndume ya soki kudirin tare da cewa yana da manyan matsaloli hudu, wadanda suka haɗa da:
1. Rashin dacewar lokacin
2. Sabawa tsarin tarayya
3. Karin harajin VAT
4. Rashin tattaunawa mai zurfi
Tirjiyar ’yan majalisar Arewa ga Tinubu
'Dan majalisa daga mazabar Birnin Gwari/Giwa na jihar Kaduna, Bashir Zubairu ya bayyana kudirin a matsayin “tilastawa” wanda zai yi wa yankin Arewa illa.
“Muna shirye don yakar duk wani yunkuri na kakaba mana kudirin zai cutar da miliyoyin ’yan Najeriya. Wannan faɗa ne da za mu yi da ƙarfi domin kare muradunmu,”
- Bashir Zubairu
Rahoton Trust Radio ya ce dan majalisa daga Rano, Kibiya, da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum ya ce ’yan majalisar Kano sun haɗa kai wajen adawa da kudirin, yana mai cewa,
“Wannan kudiri zai cutar da Arewa, kuma za mu yi faɗa da shi a lokutan muhawara da bayan ta.”
Haka nan, Dr Ghali Mustapha Tijjani daga mazabar Gaya da Ajingi ya bayyana kudirin a matsayin wani mataki mai tsauri da bai dace da yanayin rayuwar talakawa ba.
Ra’ayoyi daga sauran yankuna
A gefe guda, Sanata Enyinnaya Abaribe daga Abia ta Kudu ya bayyana cewa kudirin ba zai tsallake yadda yake ba, yana mai cewa za a sake fasalta shi kafin ya samu amincewa.
Haka zalika, Babajimi Benson daga mazabar Ikorodu na jihar Legas ya kare kudirin, yana mai cewa gyaran harajin yana nufin tabbatar da cewa kowace jiha ta bunƙasa tattalin arzikinta.
Ya kuma tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ba zai ɗauki wani mataki da zai cutar da yankin Arewa ba, kasancewar shi ne ya ba shi babbar gudummawa a zaɓen 2023.
Gboyega Nasiru Isiaka daga mazabar Yewa/Imeko-Afon ya jaddada mahimmancin gyaran haraji, yana mai cewa dokokin haraji na yanzu suna bukatar gyara domin dacewa da yanayin zamani.
Tinubu ya gana da shugaban Rwanda
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fadi matakan da ya kamata a dauka domin farfado da tattalin Afrika.
Bola Tinubu ya fadi haka ne yayin ganawa da shugaban kasar Rwanda a kasar Qatar inda ya ce Afrika na da duk abin da take bukata domin cigaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng