Siyasa Rigar 'Yanci: Gwamnoni 5 da Za Su Iya Sauya Sheka Kafin Zaben 2027
Yayin da ake yunƙurin fara kaɗa gangar zaɓen 2027, jita-jita ta fara yawo kan gwamnonin da za su iya sauya sheƙa daga jam'iyyunsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jita-jitar ta nuna cewa gwamnonin jam’iyyun adawa guda biyar waɗanda ke a wa’adin farko, na iya barin jam'iyyun da aka zaɓe su a kai.
Wasu gwamnoni za su iya sauya sheƙa
Jaridar Leadership ta ce gwamnonin jihohin Abia (Alex Otti), Enugu (Peter Mbah), Delta (Sheriff Oborevwori), Rivers (Siminalayi Fubara), da Akwa Ibom (Umoh Eno), sai da suka fito suka yi magana kan jita-jitar sauya sheƙarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin dai an yaɗa jita-jitar cewa suna shirin komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Duk da yake Mbah, Fubara, Eno, da Oborevwori suna cikin jam’iyyar adawa ta PDP, Otti yana a jam'iyyar LP.
Abin mamaki, dukkan jam’iyyun biyu suna fama da rikice-rikicen cikin gida bayan zaɓen 2023, wanda har yanzu aka kasa kawo ƙarshensa.
Meyasa ake jita-jitar sauya sheƙar gwamnoni?
Majiyoyi sun bayyana cewa wasu daga cikin gwamnonin ana matsa musu lamba a ɓoye don su shiga APC mai mulki.
Wasu kuma rikicin da ake yi a cikin jam’iyyunsu, ya sa suke duba yiwuwar shiga wata jam'iyyar da za ta ba su damar samun wa’adi na biyu.
Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya a 1999, gwamnonin jihohi fiye da 20 sun sauya sheƙa daga jam’iyyarsu zuwa wata.
1. Gwamna Alex Otti (jihar Abia)
A jihar Abia, an fara nuna shakku game da biyayyar Gwamna Alex Otti ga jam’iyyarsa lokacin da ya goyi bayan ƴan takarar jam’iyyar ZLP a zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Jita-jitar cewa zai bar jam’iyyar LP ta ƙara yawa ne a lokacin bikin ƙaddamar da filin jirgin sama na Abia, inda ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Gwamna Otti zai koma APC.
Haka kuma, mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya sha yin kira ga Gwamna Otti da ya shigo APC.
Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mambobi biyar na jam’iyyar LP a majalisar wakilai ne suka sauya sheƙa zuwa APC.
Sai dai, wani babban jami’in gwamnati, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce bai san da irin wannan matsin lamba ba.
2. Gwamna Siminalayi Fubara (jihar Rivers)
A jihar Rivers, ana raɗe-raɗen Gwamna Siminalayi Fubara zai bar PDP bayan ya kasa ƙwace ikonta daga hannun ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Amfani da jam’iyyar APP da Gwamna Fubara ya yi a zaɓen ƙananan hukumomi, ya ƙara ƙarfafa jita-jitar cewa zai iya barin PDP kafin zaɓen 2027.
Sai dai kwamishinan yaɗa labarai na Rivers, Warisenibo Joe Johnson, ya ce Gwamna Siminalayi Fubara ba shi da wani shirin barin PDP zuwa wata jam’iyya, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
3. Gwamna Umo Uno (jihar Akwa Ibom)
A jihar Akwa Ibom, an fara yaɗa jita-jitar cewa Gwamna Umo Uno Eno zai iya tattara ƴan komatsansa daga PDP zuwa APC.
Kusancin da ke tsakanin gwamnan da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wanda shi ne ɗaya daga cikin manyan shugabannin APC, ya sa ake zargin cewa yana iya komawa APC.
PDP a jihar Akwa Ibom ta musanta wannan ikirari, tana mai kiran hakan da aikin masu yaɗa jita-jita kawai.
Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Elder Aniekan Akpan, ya musanta batun sauya sheƙar yana mai cewa hakan kawai shaci-fadi ne daga masu yaɗa jita-jita.
4. Gwamna Peter Mbah (jihar Enugu)
A jihar Enugu, akwai raɗe-raɗin cewa rikicin cikin gida na PDP a matakin ƙasa zai iya sa Gwamna Peter Mbah ya sauya sheƙa.
Sai dai mai magana da yawun PDP a jihar Enugu, Uchenna Obute Udi, ya bayyana jita-jitar cewa yawancin mambobin jam’iyyar na shirin sauya sheƙa zuwa APC a matsayin ƙarya.
Ya bayyana Gwamna Peter Mbah, a matsayin shugaban PDP a jihar Enugu da yankin Kudu maso Gabas.
5. Gwamna Sheriff Oborevwori (jihar Delta)
Shugabannin PDP a Delta, ƙarƙashin kungiyar Concerned Leaders of PDP, sun yi ƙorafi kan dangantakar Gwamna Sheriff Oborevwori da shugabannin APC.
Jaridar The Nation ta ce shugabannin jam’iyyar sun zargi gwamnan da ɗasawa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, domin samun wa’adi na biyu a matsayin gwamna.
Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Delta, Sir Festus Ahon, ya ce babu gaskiya cikin wannan zargi da shugabannin PDP suka yi na cewa Gwamna Oborevwori na shirin sauya sheƙa zuwa APC.
Ya bayyana cewa jita-jitar ƙarya ce tsantsagwaronta wacce ƴan adawa suke ƴaɗawa.
PDP ta cika baki kan zaɓen 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya taɓo batun zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sakataren na jam'iyyar PDP na ƙasa ya cika bakin cewa mulki zai bar hannun APC a zaɓen 2027 ya dawo hannun PDP mai adawa a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng