Wani Shugaban Karamar Hukuma Ya Sake Nada Hadimai 130 Watanni 6 da Nadin Mutum 100

Wani Shugaban Karamar Hukuma Ya Sake Nada Hadimai 130 Watanni 6 da Nadin Mutum 100

  • Shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers ya nada hadimai na musamman guda 130 domin kawo sauyi a yankin
  • Shugaban karamar hukumar, Chijioke Ihunwo, ya yi nadin ne watanni shida bayan nada hadimai guda 100 da aka yi ta ce-ce-ku-ce
  • Nadin ya haɗa da maza da mata ciki har da Helen Nyekwere da Josephine Wogu da Daisy Worgu da Grace Amadi, tare da kira su yi aiki da gaskiya
  • Dan siyasar ya ba sababbin hadiman nasa shawara kan yadda za su gudanar da ayyukansu domin samun cigaba a karamar hukumar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Port Harcourt, Rivers - Shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Ribas, Chijioke Ihunwo, ya sanar da nadin mataimaka na musamman 130.

Dan siyasar ya yi wannan nadin ne domin sababbin hadiman su taimaka masa wurin tabbatar da kawo sauyi a karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi kauyuka suna yanka mutane da wuka, sun kashe rayuka

Ciyaman ya nada hadimai na musamman guda 130
Shugaban karamar hukuma a jihar Rivers ya nada hadimai 130. Hoto: @AmbChijioke.
Asali: Twitter

Ciyaman ya nada hadimai 100 a Rivers

Mr. Ihunwo ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba 8 ga watan Janairun 2025 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matakin ya zo bayan nadin mataimaka na musamman 100 da ya yi a watan Yulin 2024 lokacin da yake shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar.

Ihunwo yana da alaƙa mai karfi da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, wanda ya janyo surutu da dama musamman bayan rigimarsa da Nyesom Wike.

Rigimar da Wike da Fubara ke yi a Rivers

A watan Oktoban 2024, Ihunwo ya cire mutunmutumi da ke dauke da sunan tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, daga mashigar ginin karamar hukumar Obio-Akpor.

Wike, wanda yanzu shi ne ministan babban birnin Tarayya, ya fito daga Rumuepirikom ya dade yana takun-saka da Gwamna Fubara.

Rikicin siyasar Wike da Fubara ya haddasa rashin jituwa a jihar, kowanne ke fafutukar nuna karfi da iko a siyasance wanda har ta kai zaman sulhu a lokuta da dama amma a banza.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi alakarsa da El-Rufai, ya magantu kan barinsa APC da hana shi Minista

Ihunwo ya shawarci sababbin hadimai da ya nada

Hon. Ihunwo ya shawarci sababbin wadanda suka samu muƙamin da su yi aiki tukuru domin kawo cigaba a karamar hukumar.

Daga cikin wadanda aka nada akwai maza da mata har guda 130 inda Ihunwo ya bukaci hadin kansu domin samun abin da ake nema.

Ya taya su murna tare da kira gare su da su yi aiki tukuru don amfanin karamar hukumar Obio/Akpor gaba ɗaya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa nadin nasu ya fara aiki nan take ba tare da bata wani lokaci ba.

Ciyaman ya gabatar da kasafin N5.5bn a Majalisa

Kun ji cewa Shugaban karamar hukuma a Enugu ya gabatar da kasafin 2025 na N5.5bn, wanda ya zarce N4.153bn da ya gabatar a 2024.

Kasafin kudin ya maida hankali kan manyan ayyuka kamar tituna, lafiya, aikin gona da ilimi, tare da shirin inganta kudin shiga.

Kara karanta wannan

'Magana ta fara fitowa': Hamza Al Mustapha ya fadi dalilin ganawa da El Rufa'i

Gwamnan jihar Enugu ya tallafa wa karamar hukumar ta shirin Smart Green Schools, inda ake zuba fiye da N1bn a kowace mazaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.