Ganduje Ya Yi wa Kwankwaso Shagube, Ya Yi Barazanar Kwace Kano a Zaben 2027

Ganduje Ya Yi wa Kwankwaso Shagube, Ya Yi Barazanar Kwace Kano a Zaben 2027

  • Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa magoya bayan Sanata Rabiu Kwankwaso sun yi baƙin ciki da mulkin NNPP a Kano
  • Ganduje ya ce jam’iyyar APC ta shirya tsaf domin kwace mulki daga NNPP a zaɓe mai zuwa, tare da yin kira ga haɗin kai a cikin jam’iyyar
  • Ya bayyana cewa yanzu haka, da yawa daga cikin magoya bayan Kwankwaso sun ja da baya, saboda haka nasara ba zai ba su wuya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce magoya bayan Sanata Rabiu Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata, sun yi baƙin ciki da yadda jam’iyyar ta gudanar da mulki a Kano.

Kara karanta wannan

APC: El Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan jita jitar sauya sheka

Ganduje ya faɗi haka ne yayin liyafar kwanaki biyu don karamma 'yan majalisar dokokin jihar Kano na jam'iyyar APC, da aka shirya domin jinjina masu saboda gudunmawar da suke bayarwa.

Ganduje
Ganduje ya yi barazanar kwace NNPP a zabe mai zuwa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa daga cikin shugabannin da aka girmama akwai Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, Rt. Hon. Hamisu Ibrahim Chidari, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Atta, Labaran Abdul Madari, Ayuba Labaran Durum, Babangida Alasan Yakudima da Baffa Babba Danagundi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta shirya kwace mulki daga NNPP

A cikin jawabinsa da aka isar ta bakin Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, Abdullahi Ganduje ya ce jam’iyyarsa ta shirya tsaf domin kwace mulki daga NNPP.

Da yake magana kan Kwankwaso, Ganduje ya ce:

“Abin mamaki ne yadda Rabiu Kwankwaso ke da’awar yana da goyon bayan jama’a. Na rantse da Allah, da ba don matsalolin cikin gida ba, da bai yi nasara a kowanne zaɓe a Kano ba. A wannan karon, zai gane gaskiya. Wadanda suka mara masa baya a baya yanzu su na baƙin ciki da nadama. Kwankwasiyya ta ƙare, kuma ko gwamnan ba ya sanin abin da ke faruwa a kewaye da shi.”

Kara karanta wannan

2027: Shugaban NNPP na Kano ya jawo wa kansa magana mai zafi kan tazarcen Tinubu

Ganduje ya fadi shirin kwace jihar Kano

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya jaddada cewa haɗin kai shi ne hanyar da za ta kai jam’iyyar ga nasara a zaɓe mai zuwa.

Ya kara da cewa;

“Haɗin kai ita ce kawai mafita gare mu. Wannan shi ne zaɓin da muke da shi don cimma burinmu. Allah ya riga ya shiga cikin lamarinmu; gwamnatin yanzu tana ɓata jihar, kuma muna jiran lokacin da ya dace. Zaɓe na gaba zai kasance kamar ɗaukar kaza daga kan ƙwai,” in ji shi.

Ministan Tinubu ya goyi bayan APC

Karamin Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya jaddada cewa haɗin kai shi ne babban ƙalubalen da APC za ta kawar a Kano don samunnasara.

Ya ce;

“Batun zaɓe ba matsala ba ce gare mu. Da za a yi zaɓen yau, ba mu da abin tsoro. Mun ci wanda ya gabata; kawai Allah bai ba mu nasara ba. Mu yi addu’a kuma mu hade guri guda.”

Kara karanta wannan

'Kano ta Tinubu ce": Bichi ya fadi shirin da suke yi a 2027, ya yaba wa Ganduje

Jagorancin da ke yanzu a jihar ba shi da tasiri, kuma babu wanda yake jin daɗin mulkinsu.”

Ata ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa fifita Kano a cikin ayyukan ci gaban ƙasa.

Jagororin jam'iyyar APC sun dira a Kano

A baya, kun ji cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci bikin daurin auren 'ya'yan shugaban jam'iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, wanda aka gudanar a masallacin Al-Furqan a ranar Asabar.

Shettima ya samu tarba daga manyan mutane a Kano, ciki har da mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, Sanata Barau Jibrin, da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasir Yusuf Gawuna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.