Shugaban FIRS Zai Ajiye Kujerarsa domin Neman Gwamna? Gaskiya Ta Fito
- Shugaban hukumar tattara kudin shiga ta FIRS, Zacch Adelabu Adedeji, ya yi magana kan jita-jitar tsaya wa takarar gwamna a jihar Oyo
- Mr. Zacch ya ce burinsa shi ne mayar da hankali kan cika ayyukan da aka ɗora masa a yanzu ba tare da shiga siyasa ba
- Adedeji ya nemi addu’a daga jama’a don samun nasarar kammala wa’adin aikin da ke gabansa ba tare da an karkatar masa da hankali ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ibadan, Oyo - Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga na Ƙasa (FIRS), Zacch Adelabu Adedeji ya mayar da martani kan rade-radin tsayawa takarar gwamna.
Adedeji ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar kujerar gwamnan jihar Oyo a shekarar 2027 ba.
Mr Zacch ya fadi burinsa a gwamnatin Tinubu
A cikin wata hira da ya yi kwanan nan a bainar jama’a, Adedeji ya ce zai mayar da hankali ne kan nauyin da aka daura masa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban FIRS, wanda fitaccen ɗan siyasa ne da aka sani sosai a jihar, ya ce ya fi mayar da hankali kan cika ayyukansa na yanzu.
Tsohon kwamishinan kudi a Oyo ya ce babban burinsa shi ne sauke nauyin da Allah ya daura masa a hukumar FIRS.
Shugaban FIRS ya musanta tsayawa takarar gwamna
“Ina son amfani da wannan dama don amsa tambayoyin mutane da yawa, ni, Zacch Adedeji, ba zan tsaya takarar zaben gwamna a 2027 ba."
"Zuwa wannan lokaci, da yardar Allah, mun yi duk abin da Allah yake so mu yi a jihar, abin da kawai nake nema shi ne addu’o’in don samun damar ƙarasa abin da nake yi, ba na son wani abu ya karkatar da hankalina.”
- Zacch Adelabu Adedeji
Gwamna Makinde ya yi sababbin nade-nade
Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya yi wasu sababbin naɗe-naɗen da ba a taɓa yin irinsu ba a tarihin gwamnatin jihar Oyo.
Gwamnan na PDP, wanda a kwanakin baya aka yaɗa jita-jitar yana shirin neman takarar shugaban kasa a 2027, ya naɗa manyan sakatarori 45.
Asali: Legit.ng