'Kano Ta Tinubu ce': Bichi Ya Fadi Shirin da Suke Yi a 2027, Ya Yaba wa Ganduje

'Kano Ta Tinubu ce': Bichi Ya Fadi Shirin da Suke Yi a 2027, Ya Yaba wa Ganduje

  • Sabon shugaban hukumar raya kogin Hadejia da Jama’are, Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana cewa Kano za ta kada kuri'a sosai ga APC
  • Bichi ya soki gwamnatin Abba Yusuf ta NNPP, inda ya ce manufofinta sun sa mutane sun daina sha'awar jam'iyyar tun kafin zaben 2027
  • 'Dan siyasar ya fadi haka a wani taro don karrama ‘yan asalin jihar da Bola Tinubu ya nada, tare da yaba masa bisa damawa da Kano a gwamnatinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sabon shugaban hukumar HJRBDA, Rabiu Suleiman Bichi, ya yi magana kan zaben 2027.

Rabiu Bichi ya bayyana cewa Kano za ta kada kuri’a sosai ga Bola Tinubu da APC a babban zaɓen 2027.

Jigon APC ya sha alwashin ba Tinubu Kano a 2027
Injiniya Sulaiman Bichi ya sha alwashin kawo Kano ga APC da Tinubu a 2027. Hoto: All Progressives Congress, @DOlusegun.
Asali: Facebook

2027: Bichi ya sha alwashin ba Bola Tinubu nasara

Bichi ya yi wannan bayani ne a Kano yayin liyafar da ƙungiyar matasan APC (CAYM) karkashin jagorancin Adamu Mukhtar ta shirya, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Bayan martanin Kwankwaso kan haɗaka, Peter Obi ya magantu kan rade radin haduwarsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da taron ne don karrama mutane uku da suka fito daga Kano waɗanda shugaban kasa Bola Tinubu ya nada.

Bichi ya bayyana cewa ana ci gaba da shirye-shiryen farfaɗo da goyon bayan matasa don tabbatar da nasarar APC da Bola Tinubu a zaɓen mai zuwa.

Bichi ya caccaki mulkin Abba Kabir da NNPP

A jawabinsa, Bichi ya soki jam’iyyar NNPP, yana cewa manufofinta sun jawo mutane sun dai na sha’awar gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Injiniya Bichi ya zargi gwamnatin Abba Yusuf da watsi da shirye-shiryen ci gaba na Abdullahi Ganduje, tare da lalata kadarorin da suka kai darajar N150bn.

“Mun gode wa shugaban kasa bisa nadin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyarmu ta ƙasa."
“Mutanen Kano sun gaji da gwamnatin Abba Yusuf, kowa yana jiran lokacin kada kuri’a don kawo canji a jihar da ba Tinubu da APC nasara."

- Sulaiman Bichi

Tsohon Minista ya yabawa mulkin Tinubu

Kara karanta wannan

Yadda aka 'tsorata' Tinubu ya ki karbar minista a gwamnatin Yar'adua

Kun ji cewa tsohon Ministan Gidaje, Dr. Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya yaba wa Bola Tinubu kan jagoranci da gyare-gyare don ci gaban Najeriya.

Gwarzo ya jinjina wa 'yan Najeriya bisa jajircewa wajen tallafa wa hangen nesa na shugaba Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.