An Fara Hada Kai da Wasu 'Yan APC cikin Tafiyar Kifar da Tinubu a 2027

An Fara Hada Kai da Wasu 'Yan APC cikin Tafiyar Kifar da Tinubu a 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa, Salihu Lukman ya bayyana cewa ‘yan adawa sun fara tattaunawa kan siyasar 2027
  • Salihu Lukman ya ce tattaunawar ta haɗa har da wasu shugabannin APC da suka ga alamar ba su da wurin zama a jam’iyyar
  • Lukman ya jaddada cewa dole ne a rungumi siyasar sadaukarwa domin ceto Najeriya daga halin da kasar ke ciki a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Salihu Lukman, ya bayyana cewa ana tattaunawa da ‘yan adawa kan samar da sabuwar tafiya kafin zaben 2027.

A cewarsa, dole ne ‘yan adawa su sauya tunani kuma su maida hankali wajen bai wa jama’a damar zaɓen shugabanni ta hanyar tsarin gaskiya.

Kara karanta wannan

"Ka fito ka faɗawa mutane gaskiya," Peter Obi ya kwancewa Tinubu zani a kasuwa

Lookman
'Yan adawa sun fara tattaunawa domin hada a 2027. Hoto: Bayo Onanuga|Salihu Lukman
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Salihu Lukman ya bayyana haka ne a cikin saƙon sabuwar shekara da ya fitar a birnin tarayya, Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sakon, ya bayyana damuwarsa kan yadda yawancin ‘yan siyasar Najeriya ke dogara kan burinsu na kai wa ga mukamai maimakon siyasa mai ma’ana.

2027: Shugabannin adawa sun fara tattaunawa

Salihu Lukman ya tabbatar da cewa wasu shugabannin ‘yan adawa, ciki har da waɗanda suka ji ba su da wurin zama a APC, sun fara tattaunawa kan samar da wata sabuwar tafiyar siyasa.

“Dole ne mu tuna wa shugabannin siyasa cewa idan har suna son nuna darajar sadaukarwa da kuma samar da jagorancin ceto Najeriya,
Ya zama wajibi su rungumi siyasar ceto kasa a matsayin hanya mafi kyau ta samar da shugabanni.”
“Yawancin ‘yan siyasar Najeriya suna dogara ne kan burinsu na son kai. Wannan tunanin na neman hana tsarin siyasa na gaskiya, wanda ke kawo matsalolin jagoranci a Najeriya.”

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

- Salihu Lukman

Lukman ya bukaci jama’a su tashi tsaye

This Day ta wallafa cewa Lukman ya yi kira ga ‘yan Najeriya su farka daga barcinsu su ɗauki makomar ƙasarsu a hannunsu.

“Ƙarfin hali da ‘yan siyasar Najeriya ke nunawa ya dogara ne kan yadda talakawa suka yi shiru kuma suka bar siyasa ga masu kiran kansu ‘yan siyasa kawai.”

- Salihu Lukman

Lukman ya ce idan har yawancin ‘yan Najeriya ba su tashi tsaye ba, za a ci gaba da samun matsaloli masu tsanani na shugabanci da tsadar rayuwa.

Ya ƙara da cewa shugabannin adawa su fahimci cewa idan har suna son ceto Najeriya, to dole ne su daina ɗaukar siyasa a matsayin hanya ta ɗora kansu kan mukamai.

PDP ta bukaci 'yan adawa su hada kai

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar PDP, Ambasada Umar Damagun ya bayyana hanyar da za su bi wajen kayar da Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

PDP: 'Abin da ya kamata Kwankwaso da ƴan adawa su yi don kayar da Tinubu a 2027'

Umar Damagun ya tabbatar da cewa dole dukkan manyan 'yan adawa su zamo tsintsiya madaurinki daya idan suna son ceto Najeriya daga hannun APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng