"Tinubu na kan Siraɗi": Peter Obi Ya Yi Magana kan Haɗaka da Kwankwaso da Atiku
- Ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023 a LP, Peter Obi ya ce babu wata yarjejeniyar ƙulla kawance da suka cimmawa da wasu jam'iyyu
- Mista Obi ya bukaci ƴan siyasa masu kishin kasa su taho a haɗa karfi da ƙarfe domin ceto Najeriya daga gurɓataccen mulkin APC
- Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce matsalar tsaro ta zama babban abin takaici, cin hanci ya ƙaru a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya ce har yanzu babu wata yatjejrniyar haɗa maja da suka cimmawa da kowace jam'iyyar siyasa.
Peter Obi ya ce kawo yanzu jam'iyyar LP ba ta cimma wata yarjeniya da NNPP, PDP ko wasu jam'iyyun siyasa kan haɗa maja a gabanin zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a safiyar ranar Alhamis lokacin da yake hira da manema labarai a Abuja, kamar yadda Channels tv ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babu wata yarjejeniya tsakaninsa da Atiku Abubakar da Obi.
Peter Obi ya yi maganar haɗa maja
Mista Obi ya bukaci duk wani mai kishin kasa ya taho su haɗa karfi da karfe wajen kayar da jam'iyyar APC, wacce ya ce ta gaza, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya bayyana matsalar tsaron da ake fama da ita a matsayin abin takaici, yana mai cewa mutane na rasa ransu ba gaira babu dalili sanadiyyar matsalar ƴan bindiga da ƴan tada kayar baya.
Obi: 'Gwamnatin Bola Tinubu ta gaza'
Ya ce har yanzu babu abin da ke raguwa a batun cin hanci da rashawa sai dai abin da ya ƙaru a karƙashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Peter Obi ya yi zargin cewa da gangan jami'an gwamnati ke almubazzaranci da kuɗin kasa ta hanyar tafiye-tafiye marasa amfani zuwa ƙasashen ketare.
Shugaban PDP ya bukaci haɗa kan ƴan adawa
A wani rahoton, kun ji cewa muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum ya ce dole sai ƴan adawa sun haɗa kai za su iya ganin bayan APC a 2027.
Damagum ya caccaki tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai cewa har yanzu ruwa ya na maganin dauɗa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng